Kare Ya Kama Uwar Gidansa Na Holewa da Saurayinta a Daki, Ya Ture Shi a Bidiyo

Kare Ya Kama Uwar Gidansa Na Holewa da Saurayinta a Daki, Ya Ture Shi a Bidiyo

  • Wani bidiyon nishaɗi ya ja hankali a soshiyal midiya, ya nuna yadda wani Kare ya kamu da tsananin kishi
  • A bidiyon, Mai Karen ta gayyaci Saurayinta kuma suna cikin rage wa juna zafi ba zato karen ya kawo musu tangarɗa
  • A cikin ɗan gajerin bidiyon, Karen ya nuna kishi kan uwar gidansa, ya je ya Bangaje mutumin ya shiga tsakani

Wani bidiyo da ya ja hankali ya ɗauki lokacin da wani Kare ya kamu da tsananin kishi yayin da ya hangi uwar gidansa tare da sahibinta a ɗaki suna rage zafi.

A cikin Bidiyon na barkwanci, an ga Karen ya garzaya ya bangaje mutumin sa'ilin da ya ganshi yana sumbatar matar cikin salo mai jan hankali.

Kare ya kawo cikas.
Kare Ya Kama Uwar Gidansa Na Holewa da Saurayinta a Daki, Ya Ture Shi a Bidiyo Hoto: @iamskyhollywood
Asali: UGC

Nan take Karen ya shiga tsakani kana ya koma duba Fuskar uwar gidansa don ya tabbatar da tana nan lafiya bai cutar da ita ba.

Kara karanta wannan

Rawa Ko Hauka: Bidiyon Yadda Wani Sabon Ango Mai Zumuɗi Ya Rikito Kan Amarya Ana Tsaka da Rawa

Ma'abota amfani da kafafen sada zumunta sun bayyana ra'ayoyinsu kan matakin da Karen ya ɗauka yayin da wasu suka tafa wa Karen bisa nuna kishi da kariya a lokaci guda.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duba bidiyon anan

Martanin mutane game da Bidiyon

@davidlawrence8259 yace:

"Irin waɗan nan Karnukan na ƙasar Amurka akwai su da kwazo wurin ba da kariya ga masu su. Dole ka ji kana kaunarsu."

@lolog321 ya ce:

"Karen ya nuna irin kina dai lafiya ko na kare ki daga cutarwa."

@bluecitysea ya ce:

"Akwai abubuwa da yawa a tsakanin namiji da mace, yanzu kuma babban abokin namiji na cikinta hallau."

@perfectgentleman123_ ya ce:

"Kamar yana gargaɗinsu kar su sake irin wannan halayyar, idan suka kuma zai ɗauki mataki nan take."

@foxxyladyk ta ce:

"Haka karen gidanmu yake a ko da yaushe yana makale da Babana. Ba ya iya zama idan mamana tana sunbatar babana."

Kara karanta wannan

Bidiyon Cikin Dankareren Gidan Da Wani Matashi Ya Kerawa Kansa, Ya Ji Kayan Alatu Kamar Fadar Sarki

Kwana Hudu da Aure, Amarya Ta Kama Angonta da Yar Uwarta Suna Jin Dadi a Gado

A wani labarin kuma Wata Sabuwar Amarya ta shiga tashin hankali yayin da ta kama Ango na lalata da kanwarta a gado kwana huɗu da aurensu

Sabuwar amaryar da abun ya sosa wa zuciya, tace lamarin ya taɓa ta yadda ta koma Otal na tsawon mako ɗaya ba wanka da yawo don komai ba ya mata daɗi.

Haka zalika ta nuna ba zata taɓa yafe musu ba kuma ta garkame lambobin mahaifiyarta da surukarta saboda sun nemi ta kai zuciya nesa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262