Kudin Fito: Gwamnati ta Taba Yarda Ta Biya N1.5trn Dan Kwato N20trn - inji Fadar Shugaban Kasa

Kudin Fito: Gwamnati ta Taba Yarda Ta Biya N1.5trn Dan Kwato N20trn - inji Fadar Shugaban Kasa

  • Kwananan bayanai na fitowa kan kudin fiton da gwamnatin tarayya take samu ko kuma ta ke sanyawa kamfanoni
  • Hon. Gudaji Kazaure dan majalissa mai wakiltar mazabar kazaure/Roni/Gwiwa da 'Yan-Kwashi yace a iya kudin fiton cajin mu'amalar kudi a bankuna an samu N89trn daga shekarar 2013 zuwa 2022
  • Mafi akasarin kasafin kudin gwamnatin tarayya na ta'allaka ne da abinda aka samu na kudadedn fito ko kuma arzikin man fetir

Abuja: Fadar shugaban kasa ta sake yin watsi da zargin karkatar da kudaden fito da dan majalisar wakilai Gudaji Kazaure ya yi wa wasu hukumomin gwamnati.

Wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya fitar a ranar Talata ta ce zargin “marar tushe ne”.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai Shehu ya musanta ikirarin da Kazaure yayi na cewa shi ne sakataren kwamitin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa domin duba batutuwan tattara kudaden fito.

Kara karanta wannan

Gudaji Kazaure Ya Jerowa Garba Shehu Tambayoyi, Ya Yi Karin Bayani a Kan Kwamitinsu

Buhari
Kudin Fito: Gwamnati ta Taba Yarda Ta Biya N1.5trn Dan Kwato N20trn - inji Fadar Shugaban Kasa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A martani Kazaure da ya mayar wa da Mallam Garba Shehu yace Buhari ne ya kafa kwamitin a asirce kuma shugaban kasa ne kawai zai iya rushe shi. Kamar Yadda Premium Times ta rawaito

Gwamnati Ta Bada Tiriliyan N1.5 Dan Gano Tiriliyan N20

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa ya fitar, Mallam Garba shehu yace ya kamata mutane suyi watsi da yadda ake tayin yamididi kan cewa akwai kusan naira tiriliyan 89 da aka rasa.

Garban na fadin hakan ne lokacin da ya fitar da wata sanarwa da take nuna shigen irin wannan da wani kamfani yayi, yace a bashi naira tiriliyan N1.5 zan gano triliyan N20.

Sanarwar tace:

"Irin wannan akwai wasu da suka yi ikirarin cewa a shekarar 2016 akwai Naira Tiriliyan 20 da za a karba amma an gano karya ne domin duk kudin da ake ajiyewa a bankuna bai kai rabin abinda CBN ta tabbatar a bankuna ba.

Kara karanta wannan

Wata Kotu A Kano Ta Sanar Da Ranar Da Zata Yankewa Mallam Abdul-Jabbar Nasiru Kabara Hukuncin Kisa

Mun Gano ikirarin nasu karye ne, amma dai a jimlance, gwamnatin tarayya ta kashe sama da N1.5trn domin samun kudin fito tun daga hawanta a 2015 zuwa yanzu".

Sannan sanarwa ta kara magana kan ikirarin kazaure tana mai cewa:

“Hakika, idan har gwamnatin tarayya za ta iya samun Naira tiriliyan 89, za ta iya biyan dukkan basukan da take bin ta, na kasashen waje da na cikin gida da kuma dukkan basussukan da gwamnatin jihohi ke bi kuma har a samu saura ma, sama da Naira tiriliyan 10.” in ji sanarwar.

Dan Haka Maganar ma a dau ki batun bai taso ba kuma gwamnati na sane da irin abubuwa da suke gudana musamman akan kudin fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida