Katsina: ‘Yan Sanda Sun Damke ‘Yan Bindiga 2, Sun Ceto Mutum 3 da aka Sace
- Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina tayi wa wasu ‘yan ta’adda kaca-kaca inda suka arce da miyagun raunikan bindiga
- An gano cewa, ‘yan bindigan sun kai farmaki wani kauye inda suka sace Alhaji Ali da wasu mutum hudu, amma ‘yan sanda suka ceto su
- Lamarin ya faru ne a Unguwar Rinji dake kauyen Rawayau a karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina inda DPO ya jagoranci tawagar
Katsina - ‘Yan ta’adda masu tarin yawa sun tsere da miyagun raunikan bindiga bayan runduna ta musamman ta ‘yan sanda a jihar Katsina sun dakile su tare da toshe hanyar wucewar kuma suka bude musu wuta.
A hakan ne aka yi nasarar ceto mutum biyar da aka yi garkuwa da su tare da kama wasu ‘yan ta’adda biyu, Channels TV ta rahoto.
Wannan na zuwa ne bayan ‘yan ta’adda sun kai farmaki yankin Unguwar Rinji dake kauyen Rawayau a karamar Kurfi ta jihar.
‘Yan sandan sun kwato shanun sata takwas a yankin Gidan Kanya dake kauyen Sukuntuni a karamar hukumar Kankia ta jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, a takardar da ya fitar yace lamarin ya faru a ranar Litinin bayan ‘yan sanda sun samu kiran gaggawa kan cewa ‘yan ta’adda da yawansu sun kai farmaki tare da yin garkuwa da wani Alhaji Ali da wasu mutum hudu.
A daidai wannan lokacin, kamar yadda takardar tace, an yi artabun musayar wuta tsakanin ‘yan ta’addan da ‘yan sandan inda cike da nasara aka fi karfin miyagun.
A wani labari daga rundunar ‘yan sandan, a ranar 9 ga watan Disamban 2022 wurin karfe 5:30 na yamma sun samo wata mota da ake zargin ta sata ce kirar Camry L.E a kauyen Kaware dake karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina.
Motar mai launin toka mai dubu mai lambar rijista KUJ 571 TU, Abuja, an bar ya ne a babbar hanyar Katsina zuwa Kano a wani kauye.
’Yan bindiga sun kutsa masallaci, sun sace jama’a
A wani labari na daban, ‘yan bindiga sun kai hari garin Mai Gamji dake karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina.
A take suka bindige limami tare da sace jama’a masu yawa.
Asali: Legit.ng