Kotu Ta Umarci a Tasa Kwamishinan Jihar APC Zuwa Gida Gyaran Hali

Kotu Ta Umarci a Tasa Kwamishinan Jihar APC Zuwa Gida Gyaran Hali

  • Kotun jihar Zamfara ranar Litinin ta umarci a garkame Kwamishinan Noma na jihar a gidan Gyaran hali
  • Alkalin Kotun mai shari'a Bello Shinkafi yace ya ɗaure kwamishinan ne bisa raina umarnin da ta bayar
  • Alkalin yace Kotu ta ba da umarnin Dumbulum Investment su haɗa wasu manyan kadarorin gwamnati amma ya take

Zamfara - Babbar Kotun jihar Zamfara mai zama a Gusau, a ranar Litinin ta garƙame kwamishinan noma da albarkatun ƙasa na jihar, Alhaji Ibrahim Magayaki, bisa rashin ɗa'a ga Kotu.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Alkalin Kotun mai shari'a Bello Shinkafi ya ba da umarnin a iza ƙeyar kwamishinan zuwa gidan Gyaran hali da ke garin Gusau.

Kotun Zamfara.
Kotu Ta Umarci a Tasa Kwamishinan Jihar APC Zuwa Gida Gyaran Hali Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Alkalin yace Kotu ta dogara da tanadin sashi na 9 na kundin dokokin Fenal Code biyo bayan matakin kwanishinan na ƙin biyayya ga umarnin Kotu.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-dumi: 'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Babban Basarake Mai Martaba a Jihar Zamfara

Mai Shari'a Shinkafi yace Kwamishinan ya raina umarnin da Kotu ta bayar a shari'ar da ta gudana tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da kamfanin Dumbulum Investment.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Alƙalin, Dumbulum Investement sun samu sahalewar Kotu na haɗa wa da wasu kadarorin gwamnati cikinsu har da manyan Motoci.

Shinkafi ya bayyana ceqa duk da haka Kwamishinan Noma ya sa ƙafa ya shure umarnin kana ya sayar da wasu sassan Motocin waɗanda suna daga cikin waɗanda umarnin Kotu ya shafa.

A halin yanzun, Misbahu Salauddeen, lauyan masu kara ya shaidawa manema labarai cewa matakin ɗaure kwamishina da Kotu ta ɗauka ya samo asali ne daga bukatar waɗanda yake kare wa.

Lauyan wanda aka ɗaure, Mr M. S Sulaiman, yace Antoni Janar na jihar Zamfara bai sahale masa ya zanta da 'yan jarida ba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare, Kotun Koli Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Takarar Gwamnan APC a Zaben 2023

Daga nan sai Alƙalin Kotun ya ɗage zaman zuwa ranar 16 ga watan Disamba, 2022 domin a dawo a ci gab da zaman shari'ar.

Kotu Ta Tabbatar da sahihancin takarar Umahi a 2023

A wani labarin kuma Ta Faru Ta Kare, Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Halascin Takarar Gwamna Umahi a 2023

Kotun Koli ta kawo karshen takaddama kan tikitin takarar Sanata a mazaɓar jihar Ebonyi ta kudu karkashin inuwar jam'iyyar APC.

An jima ana kai ruwa rana kan tikitin tsakanin gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi da yar takarar da ta zo na biyu a zaɓen fidda gwanin farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262