Yadda Zaka Dakatar da Shigowar Sakonni Marasa Amfani a Wayarka a MTN, Glo, Airtel

Yadda Zaka Dakatar da Shigowar Sakonni Marasa Amfani a Wayarka a MTN, Glo, Airtel

  • Hukumar NCC ta sanar da 'yan Najeriya yadda zasu hana sakonni barkatai shigowa wayarsu daga Kamfanonin sadarwa
  • Jami'in NCC mai kula da shiyyar Enugu ya yi bayani dalla-dalla kan yadda mutane zasu dakatar
  • Ya faɗi lambar da za'a kira domin neman agaji daga mahukunta kamar yan sanda, Motar Ujila da yan kwana-kwana

Enugu - Hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) ta yi kira ga 'yan Najeriya da su yi amfani da lambar 2442 wajen kawo karshen shigowar sakonnin talla da mara amfani da kamfanoni layukan waya ke tura wa.

Shugaban hukumar mai kula da shiyyar Enugu, Ogbonnaya Ugama, shi ne ya yi wannan kira yayin da yake zantawa da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) a jahar Enugu.

Wayar Hannu.
Yadda Zaka Dakatar da Shigowar Sakonni Marasa Amfani a Wayarka a MTN, Glo, Airtel Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Mista Oguma yace a mafi yawan lokuta kamfanonin waya da VAS na tura saƙuna da kiran tallace-tallace ga kwastomominsu ba tare da mutane sun nema ba, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Jigo a Najeriya ya fusata kan kin hukunta wadanda suka kashe Deborah

Ya kuma ayyana samar da gajerar lambar a matsayin, "Kare hakkin Kwastomomi" domin su zabi abinda suke son gani ko shigowa wayoyinsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda zaka dakatar da shigowar sakonnin da baka nema ba

"Domin dakatar da sakonnin da baka son gani ta hanyar amfani da lambar 2442, ka shiga wurin tura sakonni ka rubuta 'STOP' sai ka tura zuwa 2442 daga nan ka hana turo sakonnin."
"Ko kuma ka rubuta HELP ka tura zuwa 2442 sannan ka bi matakai wurin dakatar da kalar saƙonnin da baka son gani a wayarka. Sanna zaka iya tura HELP zuwa 2442 domin ganin ko an aiwatar da zaɓinka."

- Ogbonnaya Ugama.

Mai kula da shiyyar ya kuma shawarci 'yan Najeriya su rika amfani da lambar kira kyauta 112 wajen sanar da hukumar wani abu na ujila.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Sau 5 Ina Zama da Gwamna Wike, Atiku Abubakar Ya Fallasa Inda Matsalar Take

Ya tabbatar da cewa lambar tana da saukin haddacewa da kuma tunawa sannan kira kyauta ne, sannam zata haɗa mutum da duk mahukuntan da yake son kira.

"Zaka iya amfani da lambar ka kira yan sanda, jami'an kwana-kwana, Motar Ujila ta Asibiti da hukumomin lafiya," inji shi.

Game da tsarin SIM Card Porting, Mista Ugama yace ta hanyar amfani da tsarin, Mutane zasu iya canza cibiyar sadarwa daga wannan zuwa wata ba tare da an sauya musu lambar waya ba.

Yadda EFCC ta yi gwanjon Motocin da aka kwace hannun mahaddama

A wani labarin kuma EFCC Ta Yi Gwanjon Motocin da Aka Kwace a Hannun ’Yan Rashawa a Jihar Legas

Hukumar yaki da masu kwashe tattalin arzikin ƙasa EFCC tace ta yi gwanjon daruruwan mutoci da ta kwace hannun mutane bisa doka.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ya fitar, yace sun fara gwanjon a jihar Legas daga ranar 6 ga watan nan, kuma zata faɗaɗa lamarin zuwa sauran rassanta na ƙasa.

Kara karanta wannan

ICPC Ta Kama Wani Jami'in Rundunar Tsaro Ta NSCDC Da Zamba Cikin Aminci

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262