'Yan Boko Haram Sun Shiga Tasku Yayin da Mayakan ISWAP Suka Kai Hari a Sambisa
- 'Yan ta'addan Boko Haram sun tsere yayin da abokansu na ta'addanci suka kai musu harin daukar fansa
- Boko Haram ta hallaka mata 33 na 'yan ISWAP a cikin watannan, lamarin da ya kai ga mummunan martani
- 'Yan ta'addan na ci gaba da hallaka juna tun bayan da aka samu rabuwa tsakaninsu, sojoji kuma ragargazarsu
Bama, jihar Borno - ‘Yan ta’addan Boko Haram sun tsere yayin da abokansu ‘yan ta’addan ISWAP suka kai musu farmaki a yankin Gaizuwa a karamar hukumar Bama ta jihar Borno, kafar labarai ta Zagazoka Makama ta tattaro.
An tattaro cewa, ‘yan Boko Haram din sun gudu ne yayin da Ba’ana Chingori na ISWAP ya jagoranci tawagar mayakansa a cikin motocin Hilux da babura ga maboyar Abu Ikilima.
A ranar 3 ga watan Disamba ne ‘yan Boko Haram suka hallaka matan ‘yan ISWAP 33 a harinsu na daukar fansan kashe kwamandansu, Mallam Aboubakar (Munzir) da wasu mayakansa 15 da ISWAP din ta kashe.
Harin da Ali Ngulde, kwamandan Boko Haram mai shekaru 25 ya kai tare da wasu biyar da suka hada da Muke daga tsaunin Mandara, Ali Ghana daga Nguri, Abbah Tukur daga Mantari, Maimusari, Abu Isa da wani da ba bayyana sunansa ba ya kai ga mutuwar jiga-jigan ISWAP.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yadda ISWAP ta kawo farmaki maboyar Boko Haram
Karfin mayakan ISWAP da suka kai harin ya kai akalla yawan sojoji 320, 250 daga cikinsu dauke da bingogi AK47, sun zo da motoci 8 da kuma babura 50.
Zagazoka Makama, wani masani kuma mai sharhi kan lamuran tsaro ya ce, ‘yan ta’addan Boko Haram din sun tsere yayin da suka ga karfi da yawan mayakan ISWAP da suka dumfaro su.
Ya kuma bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun bar ‘ya’yansu da matansu a sansanoninsu a yayin tserewa daga maboyar.
Da yake magana da matan, Chingori ya gargadi mayakansa da kada su taba mata da kananan yara, lamarin da ya ba da mamaki ga wadanda ke tunanin harin na daukar fansa ne kan kashe matan tsagerun ISWAP.
A cewarsa:
“Bai kamata mu farmaki matansu ba kamar yadda suka yi mana.”
Ya kuma bayyana abin da Boko Haram suka yi na hari kan matansu a matsayin lusaranci da ragwanci.
Ya kuma bayyana cewa, duk inda ‘yan ta’addan suka shiga, za su tsamo su kana su tabbatar sun hallaka su.
Ana ci gaba da samun rikice-rikice tsakanin ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP a jihar Borno da tafkin Chadi.
An yi turnuka tsakanin Boko Haram da ISWAP kwanakin baya, inda aka kashe 'yan ta'adda tabkwas nan take.
Asali: Legit.ng