Tashin Hankali Yayin da Aka Tsinci Gawar Wata Budurwa Cikin Yanayi a Jos
- Mutane sun shiga tashin hankali da ruɗani bayan gano gawar qata matashiyar budurwa a wurin wankin mota a Jos
- Rahotanni sun nuna cewa mamaciyar mai suna Ruth a takaice ta shiga hannun tsagerun ne yayin dawowa daga wurin aiki
- Lamarin ya harzuƙa matasan yankin amma jami'am tsaro sun yi hanzarin zuwa wurin kana suka kwantar da hankali
Jos, Plateau - Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a jiya Lahadi ne aka tsinci gawar wata matashiyar budurwa a Jos, babban birnin jihar Filato.
Gawar budurwar wacce aka gano sunanta Ruth a taƙaice, an tsince ta ne a wurin wankin mota da ke bayan wani gidan mai a kusa da Farin Gada Bridge 1, ƙaramar hukumar Jos ta arewa.
Bayanai sun nuna cewa an ci zarafin mamaciyar kafin daga bisa ni aka kashe ta ta hanyar daɓa mata wani abu.
Ikon Allah: Bidiyon wani gidan tuwo mai ban mamaki, inda attajirai ke fakin motocinsu su kwashi girki
Wakilin jaridar ya tattaro cewa yanayin da aka tsinci gawar ya nuna an samu tirjiya daga wurinta kafin rai ya yi halinsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Lamarin dai ya ɗaga hankulan mutane a yankin, matasa sun fito zuwa wurin da aka gano gawar, don ganin menene ainihin abinda ya faru.
Ana haka ne, matasan suka yanke hukunci kan abin ya faru Kuma irin haka ka iya ta da rikicin ƙabilanci da Addini.
A halin yanzu cikin hanzari jami'an tsaro suka garzaya wurin suka dawo da komai kan hanya kafin lamarin ya kai ga ɓarkewar rikici.
Yayin da aka tuntuɓe shi, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Filato, Alabo Alfred, ba'a same shi ba balle a ji ta bakin hukumarsu.
An gano cewa Mamaciyar, Ruth na zaune a yankin Zaruma kuma ba ta jima da samun aiki ba a yankin Rayfield dake Jos makon da ya gabata.
Rahotanni sun ce waɗanda suka aikata wannan aika-aika sun farmaketa ne yayin da take hanyar komawa gida da yamma bayan tashi daga wurin aiki.
Shin dagaske ɗalibar UNIJOS ce?
Jaridar Punch tace Ruth ɗalibar Jami'ar UNIJOS ce kuma ta gama aji hudu ta karanci Kwas din yaren Turanci.
Da aka tuntubi shugaban sashin koyar da turanci na UNIJOS, Farfesa Jeff Doki, yace mamaciyar ta kammala bincike tana jiran a tura ta bautar ƙasa watau NYSC.
"Bayanan da na samu sun nuna yarinyar da aka ƙashe jiya a farin Gida ɗalibarmu ce dake gyara Kwas din da ta faɗi kafin tafiya bautar ƙasa." inji shi.
A wani labarin kuma Kansila da Wani Mutum Guda Sun Mutu a Wani Rikicin Kabilanci a Jahar Ondo
Wani rikici da ya barke tsakanin wasu garuruwa biyu ya yi sanadin rasa rayuka biyu da ƙona gonakin jama'a ba adadi a jihar Ondo.
Hadimin gwamnan Ondo kan harkokin tsaro yace rikicin ya jima tsakanin garuruwan biyu kan mallakin gonaki.
Asali: Legit.ng