Na Yi Allah Wadai da Kisan Deborah, Ɗalibar da Ta Zagi Annabi a Sokoto, Atiku
- Ɗan takarar shugaban kasa karkashin inuwar PDP, Atiku Abubakar, yace ya yi Allah wadai da kisan Debotah tun a wancan lokacin
- Yayin da ya bayyana a shirin tattaunawa da yan takara yau Lahadi, Atiku yace da farko yace a goge daga baya ya sake sabon rubutu
- Fusattatun matasa sun kashe Deborah, ɗalibar kwalejin Shehu Shagari bisa zargin ta zagi fiyayyen halitta SAW
Alhaji Atiku Abubakar, mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iyyar PDP ya sake yin Allah wadai da kisan Deborah Yakubu a kwalejin jihar Sakkwato.
Idan baku manta ba, Deborah, ɗalibar dake aji na biyu a kwalejin Shehu Shagari ta rasa rayuwarta ne hannun fusatattun matasa bayan zarginta da taɓa martabar Annabi Muhammad (SAW).
Atiku ya sake magana kan batun ne ranar Lahadi a wurin shirin tattaunawa da 'yan takara, wanda Channels tv da wasu ƙawayenta suka shirya.
Ko meyasa ɗan takarar PDP ya share rubutun Allah wadai a shafinsa?
Atiku yace ya share rubutun farko da ya yi a shafinsa kan kisan Deborah ne saboda ba da yawonsa a saki rubutun ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakin Atiku na Allah wadai da kisan Deborah da kuma goge rubutun ya haddasa cece-kuce da mahawara mai zafi tsakanin 'yan Najeriya.
Amma ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP yace ya yi Allah wadai da kisan ɗalibar a rubutun da ya biyo bayan wannan a shafinsa.
"Na umarci a goge rubutun saboda ba da yawu na aka yi ba kuma na saba sai na amince ake saki. Saboda haka ba da izina na ba nace a share, idan kun duba rubutu na na gaba na yi Allah wadai da kisan."
"A addinin Musulunci babu wurin da aka ce haka nan kawai ka raba wani da rayuwarsa, babu wurin, akwai matakan da aka tsara."
- Atiku Abubakar.
A wani labarin kuma Atiku Ya Bayyana kokarin da ya yi na ganin sun haɗa kai wuri guda da tsagin gwamna Wike a jam'iyyar PDP
A wurin hirar tattaunawa da Channels ta shirya, ɗan takarar shugaban kasan yace sau biyar yana gana wa da gwamnan Ribas amma ba wani sakamako mai kyau.
Tsohon mataimakin shugaɓan ƙasa na zango biyu yace a halin yanzun ɓangarensa ya yi iya yinsa yana jiran su Wike su yanke hukunci.
Asali: Legit.ng