Yadda Wata Mata Ta Suma A Wani Otel Bayan Da Wanda Zai Aureta Ya Kamata

Yadda Wata Mata Ta Suma A Wani Otel Bayan Da Wanda Zai Aureta Ya Kamata

  • Wata mata da take bin maza, ta suma a wani otel bayan da wanda zai aureta ya kamata
  • Matar ba ta san cewa mutumin da za ta yi hulɗa da shi hadin baki ne da wanda zata aura ba
  • Mutumin ya hada baki da wani dan gwada amintartakarta, amma ta fada tarkonsa, bayan wanda zasuyi masha'ar yayi mata alkawarin N200,000.

Wata ma’abociyar amfani da shafin Twitter ta bayyana labarin wata mata da ta suma a otal bayan da aka kama ta tana kokarin cin amanar wanda zata aura.

Wani Josh ne ya wallafa labarin wanda ya ce mutumin da abin ya shafa babban dan uwansa ne da ke son yin aure. Rahotan legit.ng

A cewar Josh, dan uwansa ya kwashe watanni 6 yana soyayya da yarinyar inda a karshe ya yanke shawarar zai aure.

Kara karanta wannan

Aure Daɗi: Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Maƙale Wa Mijinta, Ta Hana Shi Rawar Gaban Hantsi

Mata Da Saurayi
Yadda Wata Mata Ta Suma A Wani Otel Bayan Da Wanda Zai Aureta Ya Kamata Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Josh ya ce dan uwan ​​nasa ya dade yana yiwa yarinyar kyautuka , yana ba ta wayoyinta masu tsada da sauran abubuwa.

Ta fadi Jarabawa Sabida N200k

Mutumin ya ce yana so ya gwada amincin matar da yake so ya aura, dan haka kuma ya yanke shawarar gwadata.

Matar ta hadu da wata mata kuma ta ce zata hada ta da wanda zai bata N200,000 idan ta amince, kuma nan take ta amince.

Sai dai kash mutumin da zata hadu dashi a otel din shine angonta.

Lokacin da ta isa otal dan ta hadu da mutumin da za suyi masha'ar, sai ta ga wanda zata aura kuma nan take ta suma.

Al'amura sun kara ta'azzara mata ne, bayan ta fadawa wanda zata aura cewa zata je kasuwa don siyan wani abu.

Kara karanta wannan

"Shekarar 9 Muna Soyayya, Kuma Na Fi Shi Albashi": Budurwa Ƴar Shekara 34 Mai Digiri Ta Biya Wa Kanta Sadaki

Labarin ya jawo tsokaci da yawa daga masu amfani da Twitter.

Abinda ma'abota amfani da shifin Twitter suke cewa:

@Adeyanjubayomi yace:

"Wani lokaci ba wai shaidan ne yake batar da mu ba, mu da kanmu shaidanu ne."

@itieubong yayi sharhi da cewa:

"Abu mafi wahala a rayuwar namiji/mace shine zabar abokiyar/abokin zama."

@gisthaphy ya ce:

"Da fatan bata ga laifin shaidan ba, sabida itama ba abin arziki zatai ba".

Mutum ya rasa matar sa saboda Filawa da Dabino

A wani labarin mai kama da wannan, Legit.ng ta ruwaito cewa wata mata ta rabu da mijinta bayan sabida ya kasa kula da ita.

Matar ta ce mijin nata baya fita da ita kullum domin siyayya ko yawan shakatawa.

Mutumin ya amince da gazawarsa kuma ya ce ba zai iya kashewa matar kudin da ta ce ya ringa kashe mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida