An Cafke Wani Haruna Da Ya Bi Kawunsa Ɗan Shekaru 80 A Bauchi Har Gida Ya Kashe Shi Kan Zargin Maita
- Yan sanda sun kama wani mutum, Haruna Ezekiel da ake zargi da kisan kai a kauyen Gongo a jihar Bauchi
- Haruna ya halaka kakansa ne kan zarginsa da shigar da dansa cikin maita bayan ya bashi nama ya ci, hakan yasa ya garzaya ya tunkari kawun
- Wasu mazauna kauyen ne suka kai wa yan sanda rahoto bayan sun ga hayaki na fitowa daga gidan mamacin
Jihar Bauchi - Yan sanda sun kama wani mutum mai suna Haruna Ezekiel, kan kashe kawunsa dan shekara 80, Sunday Saleh, tare da binne shi a wani kabari mara zurfi kan zargin maita.
Yan sanda sun zargi Ezekiel, dan shekara 35, da kashe kawunsa na shekara 80 a kauyen Gongo da ke karamar hukumar Tafawa Balewa kan zarginsa da shigar da dansa cikin maita, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil, ya ce wani mazaunin garin dan shekara 44 ne ya kai korafi hedkwatar yan sanda da ke Tafawa Balewa a ranar 6 ga watan Disamba ya ce ya ga hayaki na fitowa daga gidan marigayin.
Ya yi bayanin cewa mazaunin kauyen ya gano Ezekiel a gidan kuma ya gano cewa ya kashe shi ya kona gawar sannan daga bisani ya haka kabari mara zurfi ya birne gawar bayan gidan da ya kona, Sahara Reporters ta rahoto.
Dalilin da yasa wanda ake zargi ya kashe kawunsa
Wakil ya yi bayanin cewa an fada wa wanda ake zargin cewa marigayin ya bawa dansa nama kwanakin baya, kuma ya same shi daga baya ya fada masa cewa naman na shiga maita ne sannan ana bukatar ya halaka mahaifinsa (wanda ake zargin) kafin ya shiga maitan.
Emefiele Yana Amfani Da Matsayinsa Don 'Azabtar' Da Yan Siyasa, Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada Aji Ya Yi Zargi
Wakil ya ce:
"Bayan jin hakan ne wanda ake zargin ya fusata ya tafi wurin marigayin don ya tunkare shi kan batun, dama ya dade yana zarginsa da maita."
Matashi dan shekara 25, Danlami, ya halaka mahaifinsa a Plateau
The Punch ta rahoto cewa yan sanda a jihar Plateau a ranar Juma'a suyn tabbatar da cafke wani Bernard Danlami, dan shekara 25 kan halaka mahaifinsa a karamar hukumar Mangu.
Kwamishinan yan sandan jihar Filato, Onyeka Bartholomew, ya tabbatarwa manema labarai hakan yayin da ya ke jawabi kan ayyukan hukumar a hedkwatar yan sanda a Jos.
Asali: Legit.ng