Bayan Kashe Naira Biliyan 1.6 Wajen Gina Gada Shekara UkuTa Fara Tsagewa
- Aikin gadar da aka fara a jihar Legas 'karkashin tsohon gwamnatin gwamnan jihar Legas Akinwumi ambode ya tsage tun kan a gama
- Gadar an fara yin aikinta ne da zammar ta samar tare da saukakawa al'ummomin Legasa saukin zirga-zirga da cunkoson ababen hawa
- Zargin dai aikta aiki marasa karko a Nigeria na samu wajen zaman kammala kwangila daga wajen dan kwangila da kuma gwamnati bayan anga aikin
Lagos: A ranar 15 ga Mayu, 2019, Akinwunmi Ambode, tsohon gwamnan Legas, ya kaddamar da aikin gina gadar da za ta hada al’ummar Ayobo-Ipaja da Egan-Igando a yankin kananan hukumomin Igando-Ikotun na jihar.
Manufar ƙaddamar da aikin shine rage cunkoso da zirga-zirga tare da inganta rayuwar mazauna yankin. Bayan shekaru uku, TheCable ta ziyarci yankin domin tantance irin aikin da aka yi.
Yayin da wakilin jaridar TheCable ke bin hanyar da gadar take, ya lura da yadda jami'an gyaran hanyar ke hana mutane bi ta wajen tare da nuna musu su bi ta kasa wanda kuma sai an biya N50 a matsayin kudin wucewa.
Wani mazaunin Ayobo-Ipaja, Macbeth Orji, ya ce jinkirin da aka samu wajen kammala aikin ya sanya tafiye-tafiye zuwa Igando da kewayen yankin wahala.
Sakamakon rufe gadar tasa mutanen yankin 'kir'kirar gadar katako kuma suke amsar N50 ga duk wanda zai 'ketara ta.
“Yanzu, N50 ba ita ce matsalar ba, amma kasancewar gadar katako ta yi nisa da inda nake zuwa shine matsalar,” in ji wata mazauniyar yankin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Al’ummar yankin sun ce dan kwangilar ya toshe bangarorin biyu na titin a wurin da aka gina gadar, lamarin da ya sanya jama’a cikin damuwa. Al'ummar sun ce yi kokarin jawo hankalin dan kwangilar kan batutuwan, amma bai saurare mu ba.
“Ba za mu iya komawa wurinsa kawai ba saboda ya gaya mana maganar da ya fada mana a baya. Yakamata gwamnatin jihar Legas ta tura wakilanta zuwa wurin aikin dan duba yadda aikin yake".
...Suka ce
Nawa Aka Kashe Wajen Gadar
Wata takarda mai dauke da wasu basussuka da jihar Legas wanda aka samu daga shafin yanar gizon gwamnatin ya nuna a watan Mayun 2019, an yi niyyar fitar da Naira biliyan 1.59 don gina gadar hanyar Egan-Ayobo.
Lokacin da TheCable ta ziyarci wurin da ake ginin a ranar 2 ga Oktobata lura da yadda wajen ya zama wani kwatami kuma wajen da yara ke amfani da shi domin kamun kifi.
Yadda Gadar Ta Tsage
Jaridar ya lura a ziyarar da ta kai a baya cewa ko da yake akwai ma'aikata, kayan aiki, da injuna a wurin, yawancin ayyukan har yanzu ba a sake su ba tsawon shekaru uku.
A yanzu halin da ake ciki, an ga yadda tsatsa ta kama ƙarafan wajen, sannan kuma ga yadda gadar ta tsatsage a 'bangaren wadda aka gina din.
Omoosebi Jibola, wani injiniyan farar hula, ya ce abu ne da ba a saba gani ba shine tsaga a kan gadar.
“Ba kasafe ake ganin tsaga ba akan gada musamman ma waddda zata dau mutane da yawa. Amma kafin mu san abin da ya haifar da wadannan tsagar, muna bukatar mu gana da jami’an da suka yi aikin,” inji Jibola.
Da yake karin haske kan dalilan tsagewar, injiniyan ya ce kayayyakin da aka yi amfani da su wajen aikin gine-ginen da suka hada da siminti da karafuna marasa inganci.
"Abubuwa da yawa na iya haifar da tsagewar, kama daga gwajin kayan aiki, gwajin inganci a kan siminti, da kuma aikin kankare," in ji shi.
A lokacin da wakilin jaridar TheCable ya ziyarci ofishin ‘yan kwangilar da ke Ikoyi, jami’in kula da ofishin ya ce manyan jami’an da ke kula da wajen basa nan.
Duk wani yunkurin ji daga gwamnatin jihar Legas ko samun bayanan kwangilar daga wajenabin ya ci tura
Asali: Legit.ng