Shugaba Buhari Ya Aike Sakon Gaisuwarsa Ga Sheikh Dahiru Bauchi

Shugaba Buhari Ya Aike Sakon Gaisuwarsa Ga Sheikh Dahiru Bauchi

  • Shugaba Buhari ya shiga sahun masu aikewa Sheikh Dahiru Bauchi bisa rashin lahiyar da yake fama
  • Babban Malamin ya kwashe gomman shekarun rayuwarsa yana karantar da jama'a ilmin addini
  • Mutane sun cika addu'a yayinda labarin rashin lafiyan Sheikh Dahiru Bauchi ya karade soshiyal Midiya

Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aike sakon gaisuwa ga Sheikh Mohammed Dahiru Bauchi bisa labarin rashin lafiyarsa da ya samu.

Buhari ya aike sakon ne ta bakin Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ranar Alhamis, 8 ga watan Disamba, 2022.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya laburta hakan a jawabin da ya fitar, rahoton DailyTrust.

Buhari ya yi addu'an Allah ya karawa babban malamin addinin lafiya bisa karantarwar da yake yiwa al'umma.

Kara karanta wannan

Sheikh Dahiru Bauchi Na Fama Da Rashin Lafiya, An Aika Masa Da Gaisuwa

Yace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ina yi masa addu'a. Allah ya kara masa lafiya."
Dahiru
Shugaba Buhari Ya Aike Sakon Gaisuwarsa Ga Sheikh Dahiru Bauchi Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Jawabin Farfesa Pantami

Minista Isa Ali Pantami wanda ya aike da sakon a madadin shugaban kasa ya bayyana cewa Shehin Malamin ya fara samun sauki.

Hakazalika ya ce Shehi ya godewa shugaban kasa bisa addu'ar samun lafiyar da yayi masa kuma yana masa addu'an nasara wajen gudanar da shugabancin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida