"Mun Rantse Ba Zamu Rabu Ba" Budurwa Ta Kaiwa Saurayinta Da Ya Haukace Abinci, Bidiyo Ya Kayatar

"Mun Rantse Ba Zamu Rabu Ba" Budurwa Ta Kaiwa Saurayinta Da Ya Haukace Abinci, Bidiyo Ya Kayatar

  • Mutane sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta a wani Bidiyo da aka ga wata budurwa na kyautatawa mahaukaci
  • Budurwar ta nuna bata jin kunyar a ganta da Mahaukacin sanye da yagaggun kaya yayin da ta kai masa abinci
  • A cewarta ba ta da wani zaɓi illa ta cigaba da kasancewa tare da shi saboda sun yi rantsuwa ba zasu taba rabuwa ba

Wani bidiyo da ya njna yadda wata budurwa ke kulawa da wani matashin mahaukaci ya haddasa cece-kuce a Soshiyal midiya.

A bidiyon da aka wallafa a shafin TikTok, an hangi budurwar ta je wurin ɗauke da abinci domin baiwa Saurayinta wanda cutar hauka ta afka ma.

Son Gaskiya.
"Mun Rantse Ba Zamu Rabu Ba" Budurwa Ta Kaiwa Saurayinta Da Ya Haukace Abinci, Bidiyo Ya Kayatar Hoto: @vivianansah223
Asali: UGC

Ba tare da ƙyamar kayan jikinsa ba, budurwar ta zauna kusa da mahaukacin kuma bata jin kunyar a gansu tare.

A wani sabon Bidiyon da aka wallafa karo na biyu, an ga budurwar na kokarin wasa da Saurayin yayin da take ɗebe masa kewa tare da nuna masa soyayya.

Kara karanta wannan

"Ina Son Ka": Budurwa Ta Faɗa Wa Ɗan Acaba Kaunar da Take Masa, Ta Ba Shi Kudi, Bidiyon Ya Girgiza Mutane

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Meyasa take zuwa wurin Mahaukacin?

Da take bayani a faifan Bidiyon, Budurwar ta rubuta cewa sun yi wa junansu alƙawari tare da rantsuwa cewa duk wuya ba abinda zai raba su sai mutuwa, shiyasa ba zata rabu da shi ba.

"Duk rintsi duk wuya mun rantse cewa ba abinda zai raba mu sai mutuwa saboda haka ba zan rabu da shi cikin kaɗaici ba," inji ta.

Ta ƙara da cewa duk da ya samu matsalar taɓin hankali, har yanzun soyayyar da take masa ba ta sauya ba.

"Kowane hali kake ciki, ina sonka."

Kalli bidiyon anan

Mutane sun jinjina mata

Kobbi JNR yace:

"Godiya bisa wannan soyayyar ta gaskiya, Allah ya miki albarka bisa wannan kyakkkyawar zuciya."

user4978732571660 yace:

"Ku dakata ku tsaya dan Allah wai dagaske ne ko wasan kwaikwayo? Idan dagaske ne Allah ya ba shi lafiya ko don ita."

Kara karanta wannan

"Ka Biyo Ni": Wata Dirarriyar Budurwa Ta Nemi Ɗan Acaba Ya Kwanta da Ita, Bidiyon Ya Girgiza Mutane

ahuofesolomon yace:

"Allah ya taimake ki babu wanda zai iya abinda kika yi gaskiya, Allah ya miki Albarka hakan ya nuna son da kike wa abokanki."

A wani labarin kuma A wani bidiyo wata budurwa ta tunkari Ɗan Acaba Ta mika masa takarda mai sakon idan ya yarda ya zo ya kwanta da ita

A bidiyon na wasan barkwanci, Ɗan Acaban wanda ke tsaka da neman halak ɗinsa ya yi kaca-kaca da takardar bayan ya karanta, ya watsar.

Kyakkwayar budurwar dake tsaye can gefe ta ga abinda mutumin zai yi ta sha mamakin ganin ko waiwayo inda take bai yi ba bayan ya yaga sakon. Mutane sun yi martani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262