Ekiti: ‘Yan Sanda Sun Gurfanar da Mutum 3 Kan Zargin Satar Akuya
- ’Yan Sanda sun gurfanarda wasu dattawa 3 kan zarginsu da satar akuya tare da mallakar wasu akuyoyin satar da tunkiya
- Kamar yadda aka gabatarwa da kotun, sun sace akuyar su uku a ranar 4 ga Dismaba wurin karfe 4 na asubahi a Iye-Ekiti
- Duk da wadanda ake zargin sun musanta aikata laifin da ake zarginsu a kai, an bayar da belinsu kan N50,000 kowanne sannan za a cigaba da shari’a
Ekiti - An gurfanar da wasu maza uku a ranar Laraba a gaban wata babbar kotun Majistare dake garin Ado-Ekiti kan zarginsu da satar lauya, jaridar The Nation ta rahoto haka.
‘Yan sanda sun mika Bamisaye Felix mai shekaru 34, Adebayo Wasiu mai shekaru 35 da Kolawole Sunday mai shekaru 42 kan zargin sata da mallaka akuyar sata, People’s Gazette ta rahoto.
‘Dan sanda mai gurfanarwa, Sifeta Bamikole Olasunkanmi, ya sanar da kotun cewa wadanda ake karar sun aikata laifin a ranar 4 ga watan Disamba wurin karfe 4 na safiya a Iye-Ekiti.
Ya zargi wadanda ake zargin da sace akuya wacce zata kai darajar N35,000 mallakin wata Oyeyemi Funmilayo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Olasunkanmi ya zargi masu kare kansun da mallakar wasu akuyoyi biyar da tunkiya daya wadanda ake zargin na sata ne.
Laifin kamar yadda tace ya ci karo da tanadin sashin na 301 sakin layi na 1 da sashi na 345 na dokokin laifukan jihar Ekiti na 2021.
‘Dan sandan mai gurfanarwar ya roki kotun da ta dage sauraron karar domin ya samu damar duba lamarin tare da gabatar da shaidu.
Wadanda ake zargin sun musanta aikata laifukan da ake zarginsu da su.
Lauyan masu kare kansu, Aduni Olanipekun ta roki kotun da ta bata belin wadanda take karewa.
Alkalin kotun majistaren, Mista Saka Afunso ya bayar da belin kowanne kan N50,000 tare da tsayayye daya kowannensu.
Ya dage sauraron karar zuwa ranar 9 ga watan Janairun sabuwar shekara.
‘Yan Sanda sun yi ram da barawon dake shigar fatalwa yana sata
A wani labari na daban, 'ya sanda na kasar Zimbabwe sun kama barawo bayan ya badda kama a zuwan fatalwa don yin sata a gidajen jama’a.
A cewar shafin Facebook, General Chiwenga Wisdom, saurayin ya kan shiga cikin gidaje cikin dare sannan ya tsoratar da mazauna gidan wadanda ke cin na kare bayan sun ganshi.
Asali: Legit.ng