Gwamnatin Buhari Ta Fadi Adadin Biliyoyin da ta Karbe a Hannun Barayi a Shekarar nan
- Gwamnatin tarayya tace dokar hana satar kudi da aka kawo a 2022, ta taimaka wajen yakar barayi
- Alhaji Lai Mohammed yace daga lokacin da aka fito da dokar nan, an yi nasarar karbe akalla N120bn
- Ministan yada labaran ya yi wannan bayani wajen karanto nasarorin da gwamnatinsu ta samu
Abuja - Gwamnatin tarayya tace ta samo akalla Naira Biliyan 120 a matsayin kudin da aka karbo a wajen ayyukan assha da ake yi a Najeriya.
Sanarwar ta fito ne ta bakin Ministan yada labarai a al’adu Alhaji Lai Mohammed a ranar Laraba. Jaridar Vanguard ta fitar da wannan rahoto.
Ministan yace an gano wadannan kudi bayan shugaba Muhammadu Buhari ya kawo dokar da za ta yaki masu samun kudi daga aikata laifuffuka.
Nasarorin da APC ta samu
Lai Mohammed ya bada albishir din ne a wajen taron manema labarai inda Ministan muhalli na kasa ya jero irin nasarorin da aka samu a mulki.
Ministan ya kira manema labarai domin zayyano cigaban da aka samu a Gwamnatin Muhammadu Buhari tsakanin Mayun 2015 zuwa Disamban nan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
People Gazette ta rahoto Ministan yada labaran yana cewa dokar da aka shigo da ita a shekarar 2022 ta taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.
Me za ayi da kudin?
Za ayi amfani da kudin ne wajen karasa muhimman ayyukan more rayuwa da ake yi a wasu jihohin Najeriya irinsu gadar Neja, titin Legas zuwa Ibadan.
A cewar Ministan labaran, da kudin da aka karbo ne za a biya ‘yan kwangila domin su karasa aikin hanyar da ta taso daga Abuja-Kaduna zuwa Kano.
Nan gaba Ministan zai yi wa jama’a bayanin inda aka kwana wajen yin wadannan muhimman ayyuka. People Gazette ta fitar da labarin nan dazu.
Yaki da rashin gaskiya
Gwamnatin Muhammadu Buhari tayi alkawarin kawo karshen matsalar rashin gaskiya, don haka aka fito da wannan doka da za ta yaki barayi.
A dalilin shigowar dokar, duk wata ma’aikata da hukumar gwamnatin tarayya ta bude asusu a karkashin bankin CBN inda ake boye dukiyar haram.
Gwamna Sanwo-Olu ya samu yaro?
Dazu aka ji labari wani ‘Dan shekara 27 mai suna Emmanuel Sanwo-Olu yace mamansa ta fada masa ba kowane mahaifinsa ba sai Gwamnan Legas.
Mista Emmanuel Sanwo-Olu yana ikirarin Mai girma Babajide Sanwo Olu ya taba samun alaka da Mahaifiyarsa shekaru da-dama da suka wuce a Delta.
Asali: Legit.ng