Kwamishinan Da Yan Bindiga Suka Sace Ya Shaki Iskar Yanci, Bayanai Sun Fito

Kwamishinan Da Yan Bindiga Suka Sace Ya Shaki Iskar Yanci, Bayanai Sun Fito

  • Kwamishinan gidaje da raya birane na jihar Benuwai, Ekpe Ogbu, ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane
  • Kwanaki biyu da suka gabata aka samu labarin kwamishinan ya faɗa hannun 'yan bindiga a kan titin Otikpo zuwa Ado
  • Matsalar garkuwa da mutane da nufin neman kuɗin fansa na ɗaya daga cikin kalubalen rashin tsaron da ya addabi arewacin ƙasar nan

Benue - Kwmaishinan gidaje da raya birane na jihar Benuwai, Ekpe Ogbu, wanda 'yan bindiga suka yi garkuwa da shi ya shaƙi iskar 'yanci.

Kanal Paul Hemba mai ritaya, mashawarci na musamman kan harkokin tsaro ga gwamna Samuel Ortom ne ya sanar da haka ranar Talata, 6 ga watan Disamba, 2022.

Kwamishina a jihar Benuwai
Kwamishinan Da Yan Bindiga Suka Sace Ya Shaki Iskar Yanci, Bayanai Sun Fito Hoto: channelsrv
Asali: UGC

Ya shaida wa gidan Talabijin ɗin Channels ta wayar tarho cewa nan ba da jimawa ba zasu fitar da bayanai cikakku kan yadda masu garkuwan suka sako shi.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kassara 'yan ta'adda, sun ragargajiya maboyar 'yan bindigaa dazukan wata jiha

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa har yanzun babu wani sahihin bayani kan ko am biya kuɗin fansa domin ceto kwamishinan ko akasin haka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ogbu ya kubuta ne kwanaki biyu bayan ya shiga hannun masu garkuwa da mutane a sanannen Junctin ɗin Adankali da ke kan titin Otukpo zuwa Ado, jihar Benuwai, arewa ta tsakiya a Najeriya.

A ranar Lahadi, gwamnatin jihar Benuwai ta sanar da cewa dakarun 'yan sanda sun gano motar Hilux Van, wacce kwamishinan ke ciki lokacin da aka farmake shi aka yi awon gaba da shi.

Gwamnatin ta sha alwashin cewa ba zata huta ba, zata haɗa hannu da dukkanin hukumomin tsaro domin kubutar da kwamishinan ba tare da maharan sun cutar da shi ba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Gwamna Ortom ya jima yana ɗora alhakin irin waɗan nan hare-haren kan 'yan fulani makiyaya, har ya kan caccaki gwamnatin shugaba Buhari bisa nuna halin ko in kula.

Kara karanta wannan

Muna Neman Tallafin FG, Mun Shiga Mugun Hali: Fasinjojin Jirgin Kasan Abj-Kd Sun Koka

Hukumar Sojojin Nigeria Zata Sauya Yadda Take Kai Hare-Harenta

A wani labarin kuma Hukumar Sojin Najeriya tace zata zauna ta sake nazari kan yadda take kai samame a dukkanin sassan ƙasar nan

Birgediya Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun hukumar sojin yace zata duba yanin ayyukanta na yaki da ƙungiyoyin ta'addanci a sassan Najeriya waɗanda suke kawo tarnaƙi a zaman lafiya.

A cewarsa akwai bukatar sauya dabaru da ƙara zafafa aikin rundunar soji domin tabbatar da zaman lafiya ya dawo a tsakanin al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262