Jadawalin Jami'oin Duniya Na 2022: Jami'oin Nigeria 10 Sun Shiga Ciki
Wata mujalla a Birtaniya da ta ƙware wajen fitar da jadawalin makarantun da suka fi kowanne a duniya ko kuma matakin karatun kowanne kwas, ta fitar da jaddawalin jami'oin da suka fi kowanne a duniya.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Mujallar mai suna Times Higher Education ta fitar da jaddawalin da ya ƙunshi jami'o'i 1,799 a cikin ƙasashe da yankuna 104.
A rahotan da Legit.ng ta wallafa tace mujallar ta yi duba ne da yadda jami'o'in suke wallafa da kuma irin taimakon da suke bayarwa wajen bincike
Wallafa miliyan 121 a cikin sama da wallafe-wallafe miliyan 15.5 mujallar ta duba, sannan ta fitar da jeringiyar. Baya ga bincike 40,000 da masana suka gudanar daga jami'o'i a fadin duniya.
“Gaba ɗaya, mun tattara bayanan sama da 680,000 daga cibiyoyi sama da 2,500 waɗanda suka bamu damar gabatar da wannan jaddawalin,” in ji Mujallar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jami'o'in Nigeria mafi ya darajara bisa kididdigar da aka yi a jadawalin ya nuna jami’o'in Ibadan da Jami’ar Legas ne a kan gaba a Najeriya.
Dukkan jami'o'in biyu, wadanda mallakar gwamnatin tarayya ne, suna a matsayi ne 401 da 500 a jadawalin.
Jami'ar Convenant, jami'a mai zaman kanta, ita ce ta uku a jadawalin a Nigeria kuma tana matsayi na 601 da 800 a duniya.
Jami'o'i 10 mafi kyau a Najeriya
S/N | Jami'o'in | Matsayinsu A Nigera | Matsayinsu A Duniya |
1 | University of Ibadan (UI) | 1 | 401-500 |
2 | University of Lagos (UNILAG) | 2 | 401-500 |
3 | Covenant University (CU) | 3 | 601-800 |
4 | Bayero University Kano (BUK) | 4 | 1100-1200 |
5 | Federal University of Akure (FUA) | 5 | 1100-1200 |
6 | University of Benin (UNIBEN) | 6 | 1201-1500 |
7 | University of Nigeria Nsuka (UNN) | 7 | 1201-1500 |
8 | Obafemi Awolawo University (OAU) | 8 | 1201-500 |
9 | Federal University of Agriculture Abekuta (FUNAAB) | 9 | 1500+ |
10 | Ladoke Akintola University Of Technology | 10 | 1500+ |
A karshe Dai Kungiyar ASUU Ta Koma Aji
A halin yanzu dai, kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta koma harkar koyo da koyarwa. Kamar yadda aka gani a tsakiyar watan oktoban da ya gabata.
Bayan ganawar da kungiyar tayi da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila a ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba, kungiyar ta janye yajin aikin da ta shafe wata takwas ta na yi
Asali: Legit.ng