CBN ta Kayyade Adadin Kudin da Za a dinga Cirewa a Bankuna Kowacce Rana

CBN ta Kayyade Adadin Kudin da Za a dinga Cirewa a Bankuna Kowacce Rana

  • Babban bankin Najeriya ya sanar da wasu sabbin ka’idoji ga bankuna kan hada-hadar kudade a fadun kasar nan wanda zai fara aiki nan da 9 ga watan Janairu mai zuwa
  • Daga cikin akwai kayyade yawan kudin da jama’a ko kungiyoyi zasu iya fitarwa a bankuna, POS da ATM a kowacce rana
  • Takardun kudin da aka umarci bankunan su dinga zubawa a ATM kuwa sun kama daga takardar N200 zuwa na kasa dasu daga watan Janairun shekara mai zuwa

FCT, Abuja - Babban bankin Najeriya ya fitar da sabbin dokokin kayyade yawan kudin da mutane da kungiyoyi zasu iya cirewa wanda zai fara aiki daga ranar 9 ga watan Janairun 2023, jaridar Punch ta rahoto.

Babban bankin Najeriya
Da Duminsa: CBN ta Kayyade Adadin Kudin da Za a dinga Cirewa a Bankuna Kowacce Rana. hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Channels TV ta rahoto cewa, kamar yadda sabuwar takardar da ta fitarwa bankuna a ranar Talata kuma ta samu saka hannun daraktan kula da bankuna, Haruna B.Mustafa, mutum daya zai iya cire N100,000 ne kadai a cikin mako daya a cikin banki, POS ko kuma a ATM yayin da kungiyoyi zasu iya cire N500,000 ne a mako daya.

Kara karanta wannan

Cristiano Ronaldo Ya Samu Sabon Kulob, Inda Zai Rika Samun N90bn a Duk Shekara

An kara da umartar bankuna da su dinga zuba takardun kudi N200 kadai zuwa kasa a ATM din su.

Takardar tace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Bayan kaddamar da sabbin takardun kudi da Shugaba Buhari yayi a ranar 23 ga watan Nuwamban 2022, dukkan bankunan kasuwa da sauran wuraren hada-hadar kudi su kiyaye da wadannan dokokin:

1. Mafi yawan kudin da za a cirewa daga banki wanda mutum daya zai iya fitarwa shi ne N100,000 sai kungiyoyi zasu iya fitar da N500,000 a kowanne mako. Kudin da za a fitar sama da hakan za a caji kashi 5 ga mutum ko kashi 10 ga kungiyoyi.

2. Cek sama da N50,000 ba za a iya biya ba yayin da kololuwa wanda shi ne N10,000,000 har yanzu dokarsa tana nan.

3. Mafi yawan kudin da za a fitar daga ATM a kowanne mako zai kasance N100,000 yayin da N20,000 zata zama mafi yawa a rana daya.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Cukuikuyi Matashin Yana Tuka Ferrari ta Bogi, Zasu Gurfanar Dashi

4. Takardun kudi daga N200 zuwa kasa ne kadai za a dinga zubawa a ATM din bankuna.

5. Mafi yawan kudin da za a iya cirewa a POS zai kasance N20,000 a kowacce rana.

CBN ta sanar da sauya takardun Naira

A wani labari na daban, shugaban Babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya sanar da cewa za a sauya takardun kudin Najeriya.

Takardun kudin da Shugaba Buhari ya yarje a sauya sun hada da N200, N500 da N1000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng