Kwana Daya Bayan Ya Ci N1m, Dan Najeriya Ya Sake Lashe N2m A Cacar Da Ya Buga Da N5K
- Rayuwar wani matashi dan Najeriya ta sauya gaba daya bayan ya taki sa'a a gidan buga caca
- Matashin ya lashe naira miliyan 2 a cacar da ya buga da N5k kacal, kwana daya bayan ya lashe naira miliyan 1
- Masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani ga nasarar da mutumin da kalamai masu dadi yayin da wasu suka nemi tallafi daga gare shi
Kafar intanet ya kaure da murna bayan wani matashi ya sanar da batun nasarar da ya samu wajen lashe naira miliyan 2 a gidan caca.
Mutumin mai suna @AmakekeJohn ya wallafa tikitin da ke tabbatar da nasarar da ya samu a Twitter yayin da ya yi godiya ga wani mai suna @joysucex_ kan gudunmawar da ya bayar wajen nasarar da ya samu a cacar.
Ya bayyana cewa ya ci naira miliyan 1 a ranar da ta gabata.
"Jiya a nan ka ci mun naira miliyan 1, yau kuma ka ci mun wani naira miliyan 2. Gobe da izinin Allah, zan ci naira miliyan 50 daga cacar ka. Ka kware dan uwa."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hoton tikitin nasa ya nuna cewa N5k ya saka a cikin cacar.
Kalli wallafar tasa a kasa:
Jama'a sun yi martani a soshiyal midiya
@hannahojoh00 ta ce:
"Dan Allah, Dan Allah ka taimaka mun da dan wani abu don na biya kudin hayar gudana. N6ok ne kuma na haura wata daya ina karatu ne a Sokoto dan Allah."
@Baba89265046 ya ce:
"Nima haka zai faru da ni...Miliyoyina za su zo kafin Janairu."
@AkanjiwasiuAbi1 ya ce:
"Na tayaka murna maigida. A dan bani wani abu na sa a aljihu."
@Joe_Akpanke ya ce:
"Woaww a ina kuke ganin wannan cacar ne."
@ElfMacarthy ya ce:
"Na ga cacar amma babu kudin bugawa, talauci yayi kyau. Bari na ci gaba da tafi da taya wadanda suka yi nasara murna har sai ranar da abun ya kai kaina..."
Matashi ya yi godiya ga Allaha a masallaci bayan ya lashe makudan kudade a caca
A wani labarin kuma, wani matashi ya lashe zunzurutun kudi har naira miliyan 38 a wani wasan caca da ya buga.
Jim kadan bayan ya yi nasara, sai aka gano matashin yana alwala tare da shiga masallaci domin godiya ga Ubangiji.
Asali: Legit.ng