Yaro Da Kudi: Matashi Dan Shekaru 16 Ya Baro Dalleliyar Mota, Hotunan Sun Yadu
- Wani matashi mai suna Isaiah Salanje ya siya motarsa ta farko yana da shekaru 16 a duniya
- Yayan saurayin, Gift Salanje, ya je shafin soshiyal midiya domin yin martani a kan sabuwar motar tare da aika gagarumin sako ga mutane
- Gift ya ce babu ruwan kudi da shekaru sannan cewa matsalar mutane da dama shine cewa suna bata lokacinsu wajen zuwa sharholiya
Wani mutumi mai suna Gift Salanje ya haddasa cece-kuce a Facebook bayan ya taya kaninsa mai shekaru 16 murnar siyan mota.
Gift ya wallafa hotunan matashin, Isaiah Salanje a kan motar, yana mai cewa yana matukar alfahari da shi.
"Ina matukar alfahari da kanina dan autanmu, a karshe dai ya siya motarsa ta farko yana da shekaru 16.
"Ina taya ka murna Isaiah Salanje," Gift ya rubuta.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da ya garzaya sashin sharhi, Gift ya kara da cewar kudi bai san shekaru ba. Ya bayyana cewa matsalar yawancin mutane shine cewa suna bata tsawon rayuwarsu wajen zuwa sharholiya. Ya rubuta:
"Mutane na nan suna samun kudi jama'a, kudi bai san shekaru ba, hatta dan shekara 10 na iya yin kudi.
"Matsalar shine yawancin ku kuna bata rayuwarku wajen zuwa sharholiya."
Jama'a sun yi martani
Liness Namfukwe ya ce:
"Rayuwar nan bata tafiya daidai faaaa a shekaruna na gaza hada k2000 na kudin kasar Zambiya na kammala karatuna yayin da a shekarunsa ya iya siyan mota."
Mhone Brianya ce:
"Mara sunan salanje eeeeeh na jinjina mai.
"Koda dai Allah kadai ya sani.
"Ina taya dan shekaru 16 murnar siyan babban mashin."
Es Orah Nagama Maqawa ya ce:
"Ya Allah idan kana azurta sauran mutane kada ka tsallake ni...Ya ubangiji ko da dubu 500 na kudin kasar Malawi ne zai ishe ni."
Budurwa ta mato kan wani dan achaba, gayen ya hadu matuka
A wani labarin, mun ji cewa wata matashiyar budurwa ta susuce a kan wani dan achaba da ya daukota saboda tsananin haduwarsa.
Hakan bai yi mata ba sai da ta dauki matashin bidiyo domin nunawa duniya irin tsantsar kyawun da Allah ya yi masa duk da kasancewarsa dan achaba.
Da dama sun yaba masa inda wasu suka ce ya fi wasu gayu da suka jiku cikin kudi haduwa.
Asali: Legit.ng