ASP Ya Sheka Lahira Sakamakon Arangama Tsakanin Sojojin Ruwa da ‘Yan Sanda

ASP Ya Sheka Lahira Sakamakon Arangama Tsakanin Sojojin Ruwa da ‘Yan Sanda

  • Gagarumin rikici wanda har yanzu ba a san tushensa ba ya barke tsakanin wasu sojojin ruwa da ‘yan sanda a titin Legas a ranakun karshen mako
  • Ana zargin sojojin ruwan da sharbawa ‘dan sanda wuka inda suka halaka shi a take, sun raunata wasu ‘yan sandan da kuma masu wucewa 3 da suka tsaya rabon fada
  • Tuni dai aka damke sojojin yayin da wasu 2 suka arce, an fara bincike bayan an kammala gawar ASP Abion da baiwa wadanda aka raunata taimako

Legas - Wani ‘dan sanda mai mukamin ASP a cikin ranakun karshen makon nan ya sheka barzahu bayan sun yi arangama da wani jami’in sojan ruwa a Legas tare da wasu ‘yan sanda wadanda suka caka masa wuka.

Rikicin soji da ‘yan sanda
ASP Ya Sheka Lahira Sakamakon Arangama Tsakanin Sojojin Ruwa da ‘Yan Sanda. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wasu mutum uku dake wucewa sun samu raunika daban-daban a sassan jikinsu sakamakon artabu da suka yi a birnin Legas.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Wani fitaccen sanatan Arewa ya tsallake farmakin 'yan bindiga a gidansa

Wannan rikicin ya haifar da hatsaniya mai rikitarwa wacce ta saka tsoro a zukatan masu shaguna wadanda suka tsere gudun abinda zai iya kaiwa ya kawo.

Mutane da yawa sun samu rauni yayin da jami’an sojan ruwan suka farmaki masu wucewa da suka so shiga tare da sasanci tsakanin jami’an tsaron.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani mai motar haya, Steven Ogbodeto, yace ya ga ‘yan sanda masu sintiri suna hayaniya kan lamarin da bai sani ba tare da wasu sojojin ruwa.

Yace dole ta sa ya tsaya ya ga ko zai iya sasanci a tsakaninsu amma sojan ruwan ya rikice tare da fara cakumar ‘dan sandan.

Wani jami’in ‘dan sanda wanda yayi magana da bukatar a sakaya sunansa saboda bashi da hurumin magana ga manema labarai, yace:

“Jami’in sojan ruwan ya sokawa jami’an mu wuka. Da gaggawa muka hanzarta kwashe jami’an mu tare da wasu mutum 3 masu wucewa zuwa asibitin Adeyemi amma ASP Abion bai tashi ba saboda likita ya tabbatar da cewa rai yayi halinsa. Sai dai sauran jami’an da wasu mutum 3 da aka soka an duba su tare da sallamarsu.

Kara karanta wannan

Dakarun Soji Sun Halaka ‘Yan Bindiga 20 a Niger, Sun Yi Nasarar Ceto Wasu Mutum 5

“An kama biyu daga cikin sojojin ruwan yayin da sauran biyu ba a kama su ba amma mun kai rahoto zuwa hukumomin soja domin a kamo sauran biyun.”

Yan Sanda sun magantu

Jaridar ThisDay ta rahoto cewa, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace ‘yan sandan na kan aikinsu yayin da sojojin suka farmake su.

Ya kara da cewa ana bincike kan lamarin.

Yace an mika lamarin hannun hukumar binciken manyan laifuka dake Panti a Yaba ta jihar Legas yayin da gawar mamacin aka ajiyeta.

Hukumar soji tayi magana

Sai dai mai magana da yawun sojin ruwa na yammaci, Edward Yeibo ya sanar da Daily Trust cewa cunkoson kan titi ne ya hada jami’an fada da wasu ‘yan sanda.

Yeibo mai matsayin kwamanda a rundunar sojin ruwa, yace a yayin haka ne ‘yan sandan tare da wasu bata garin suka fara dambatar sojojin.

Kara karanta wannan

Kano: Kasa da Sa’o’i 24 Kafin Daura Aure, Kayan Zango Sun Bace, An Sace Sadaki Wurin Daurin Aure

“Wasu ‘yan sanda sun sake bayyana a babur kuma suka fara harbi. A halin yanzu ana bincike a kai domin tabbatar da tushen lamarin. Za a bayyana makomar binciken ga jama’a.”

- Yace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng