Mafi Yawan Yara A Arewa Na Fama Da Talaucin Kayau Kamar Yadda Wani Bincike Ya Nuna

Mafi Yawan Yara A Arewa Na Fama Da Talaucin Kayau Kamar Yadda Wani Bincike Ya Nuna

  • Wani Rahoto da Aka fitar kwannan ya nuna yadda Jihohin Arewa Maso Yamma Ke fama Da Talauci da Halin Kunci
  • Jihohin Zamfara, Jigawa, Yobe Da Barno Na Daga Cikin Jihohin Da Suka Fi ko'ina Yawan Mataulata a Nigeria
  • Majalissar Dinkin Duniya Tace Yara A Yankin Gabashin Kasar Nan Na BUkatar Abinci Mai Gina Jiki Dan Magance Matsalar Yunwa Da Suke Fama Da Ita

Jigawa: Kashi 65 cikin 100 na yaran Arewa maso Yamma suna fama da talauci da yawa, inda jihar Jigawa ke matsayi mafi girma, Kamar yadda binciken 2021 Multiple Indicator Cluster Survey (MICS 6) Nuna.

Rahoton Mics 6 wanda aka kaddamar jiya a Dutse, kuma Ma’aikatar Kudi da Tsare Tattalin Arziki ta Jihar Jigawa tare da hadin guiwar ofishin UNICEF suka dauki nauyinsa.

Kara karanta wannan

Daga Karshe Dai Aminu Zai Gana Da Shugaba Buhari A Villa Yau, Bayan Aisha Buhari Ta Janye Karar Data Shigar

Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki da dama da suka hada da shugabannin siyasa, ma'aikatan gwamnati, kungiyoyin jama'a, shugabannin al'umma, shugabannin gargajiya, malaman addini da sauran masu hannu da shuni.

Yara Basa
Mafi Yawan Yara A Arewa Na Fama Da Talaucin Kayau Kamar Yadda Wani Bincike Ya Nuna Hoto: Leadership
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Raham Mohammed Farah ta ofishin UNICEF na Kano ta ce binciken da aka gudanar a shekarar 2021 ya nuna cewa kashi 73.9% na yara a Jigawa matalauta ne.

Wannan binciken ya nuna cewa ba a jihar Jigawa yara basa samun abubuwan more rayuwa. Galibin yara a jihar an tauye musu hakkinsu na rayuwa,da kuma ci gaba, injji Raham

Rahoton ya kara da cewa, yayin da jihar ta samu ci gaba yakar cutar shan inna, daga shekarar 2011 zuwa 2021, sannan ta samu gaggarumin nasara raguwar mace-macen yara ‘yan kasa da shekaru biyar da kashi 37%.

"Duk da haka, har yanzu akwai alamun da yara basu san me ake ba a jihar jigawa sabida rashin samun abunda suke bukata".

Kara karanta wannan

Aisha Buhari: Litinin Din Nan Mai Zuwa Dalbai Zasu Far Zanga-Zanga Dan A Saki Aminu

“A fannin ilimi, kashi 44% na yaran da ya kamata ace su yi firamare har yanzu sikandire ko makaratun fasaha ba su wuce kashi 2% a cikin 100% na yaran ba."

Yayin Kaddamar da Rahoton MICS6, Rahma ta yi kira na gaggawa ga shugabannin al’umma, kungiyoyin farar hula, ‘yan siyasa, ‘yan majalisar jiha da sauran masu ruwa da tsaki kan lamarin. Inda tace:

"Ya kamata a fito da dabarun inganta yanayin ci gaban bil'adama a jihar musamman don inganta rayuwar yara da matan da suka fi fama da wahala,"

Yan Nigeria Miliyan 113 Ne Ke cikin Talauci

A wani rahoto da Legit.ng ta wallafa yace: gwamnatin Tarayya Ta Sanar da cewa kaso 66 cikin dari na yan kasar na fama da talauci

wannan kaso dai ya nuna mafi yawan yan kasar na fama da halin ni'ya su a harkokin rayuwa da suka da ilimi, lafiya muhalli da sauransu

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida