Gwamnatin Nigeria Ta Gargadi Yan Kasar Kan Amfani da Manhajar Whatsapp Sabida Wasu Na Amfani Da Bayanansu

Gwamnatin Nigeria Ta Gargadi Yan Kasar Kan Amfani da Manhajar Whatsapp Sabida Wasu Na Amfani Da Bayanansu

  • Gwamnatin Nigeria Ta Shawarci Yan Kasarta Game Da Yadda Zasu Mu'amalanci Manhajar WhatsApp da ya kaurin Suna A Tsakanin Yan Kasarta
  • Wannan Shawarar Na Zuwa Ne Baya Da Wata Hukuma A Kasar Ta ce An Samu Bayanan Cewa Bayanan Masu Amfani Da Manhajar Yana Fita
  • Ana Zargin Baynan Yan Kasar Wanda Bazai Gaza Da Miliyan 9 ne Ya Fita A Rahotan Da Hukumar Tace Ta Samu

Abuja: Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa Zamani (NITDA), wata hukuma ce a karkashin ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin ta tarayya, ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan wajen amfani da manjahar WhatsApp.

A cewar NITDA, wani rahoto da aka samu ya bayana yadda wasu ke amfani da bayanan masu amfani da manhajar a fadin duniya ciki kuwa harda 'yan Najeriya.

Shugabar sashen hulda da kamfanoni da harkokin waje ta Hukumar,Hadiza Umar ce ta bayar da wannan shawarar a wata sanarwa da ta fitar a Abuja, inji rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari: Litinin Din Nan Mai Zuwa Dalbai Zasu Far Zanga-Zanga Dan A Saki Aminu

Yadda Ake Samun Bayanan Ma'abota Amfani Da Manhajar A Najeriya

A ranar 16 ga watan Nuwamba, wani dan wasan kwaikwayo ya buga wani talla a wani dandalin sada zumunta yana mai ikirarin sayar da bayanan sirri da lambobi wayar da suke da rijista a manhajar wanda adadin su yakai miliyan 487 .

An yi zargin cewa an kutsa rumbun adana bayanan masu amfani da WhatsApp daga kasashe 84, da kasar Amurka kuma aka debi bayanan mutane sama da miliyan 32.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

WhatsApp
Gwamnatin Nigeria Ta Gargadi Yan Kasar Kan Amfani da Manhajar Whatsapp Sabida Wasu Na Amfani Da Bayanansu Hoto: Getty Images
Asali: UGC

Suwaya Suka Fi Amfani Da Wayar Tarho

Har wa yau, a cikin Sanarwar ta kuma ce, wadanda suka fi mu'amala da wayar tarho a duniya sun fito ne daga yankin gabashin Afrika wato 'yan kasar Masar wanda kusan mutum miliyan 45 ke ta'ammali da ita.

Kara karanta wannan

Sojin Nigeria Sunyi Nasarar Kashe Shugaban ISAWP A Nigeria, Bayan Wani Hari Da Suka Kai

Ta Kuma bayyana sauran jerin kasashen kamar haka:

Italiya miliyan 35,

Saudiyya mai miliyan 29,

Faransa mai miliyan 20 da

Turkiyya mai miliyan 20.

A rahoton ya bayyana cewa ana siyar da bayanan yan kasar Amurka akan dala 7,000, yan Birtaniya kuma $2,500; sai yan kasar jamus akan $2,000.

Hukumar NITDA Ta Bawa Yan Nigeria Shawara

Biyo bayan wannan rahotan na samun bayanan yan Nigeria kusan mutum Miliyan Tara masu amfani da da wannan manhajar, Hukumar ta bawa yan kasa shawara.

Darakta a Hukumar Hajiya Hadiza Umar Tace:

"kusan mutum 500m ke amfani da manhajar a duniya, wanda yan Nigeria masu amfani da ita sun kai mutum 9m"
"Akwai hatsari mai girma ga duk masu amfani da wannan kafar dole su kula kuma su hankalta kan yadda zasu yi amfani da ita"
"Tace dole ne a kula da yadda ake samun bayanai barkatai, ko kuma bukatar a tura wani sako da aka samu daga wanda ba'a sani ba zuwa wasu ko wani"

Kara karanta wannan

2023: APC Ta Nesanta Tinubu da Wani Hoto da Ake Yaɗawa Tare da Shugaban Amurka, Ta Faɗi Gaskiya

Ta kuma bukaci jama’a da su tuntubi CERRT.ng ta cerrt@nitda.gov.ng ko kuma a kira +234 817 877 4580 domin karin bayani.

Martanin WhatsApp

A wani martani ga darakta a kamfanin wanda yake mallakar Meta ne yace rahoton CyberNews ba ta da wata madafa da ke tabbatar da bayanan an yi kutse tare da daukar bayanan masu amfani da manhajar WhatsApp ba.

Babu wani rahoto a hukumance da ya nuna wasu tauararin yan was ko kuma wasu kamfani na daukar bayanan amsu amfani da manhajar dan siyarwa.

Muna ba da shawara ga duk masu mu'amala da mu suyi taka-tsantsan a duk lokacin da suka sami kowane irin saƙo ko barazana ta sako ko imel.

A halin da ake ciki, Legit.ng a wani rahoton ta bayyana cewa WhatsApp na da wata sabuwar hanyar da za ta iya canja tarihin hira da ku daga Android zuwa iOS da kuma akasin haka.

Kara karanta wannan

Jami'anj Tsaro Sun ki Su Bayyana Ko A Wanne Hali Aminu Yake Ciki Baya Da Ya Shafe Mako Guda A Hannunsu

Zaka Iya Tura Bayanan WhatsApp Zuwa Wata Waya

Idan kana canza wayarka ta Android zuwa iPhone, za a iya canja bayanan ka, kamar hotuna , hirar mutum da wasu abubuwa da manhajar take kunshe dasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel