Maza Takanas Suke Zuwa Don Siyan Abinci a Wurina Saboda Dirina, Inji Mata Mai Siyar da Abinci
- Wata jajirtacciyar mata 'yar kasar Ghana mai kyawun diri da girman kugu ta bayyana yadda maza ke zuwa wurin sana'arta
- Celestina Etornam da ke siyar da garin rogo da wake a Dansoman a Accra ta ce, kwastomomi daga wurare masu nisa suke zuwa don kashe lokaci a wurinta
- Ta kuma bayyana yadda ta fara kasuwa daga kankanin jari, yanzu kuwa ta girma matuka, kamar yadda ta shaidawa SVTV Africa
Wata jajirtacciyar mata mai siyar da abinci a kasar Ghana, Celestina Etornam ta fice a kafafen sada zumunta kan zabar sana'ar siyar da abinci duk da irin diri da fadin kugu da take dashi.
Ta bayyana cewa, tana siyar da garin rogo da wake, abincin da 'yan Ghana ke yawan kira 'gob3' a yankin Dansoman na Accra a kasar.
Baya ga dandano mai dadi na abincin da take siyarwa, kwastomomi da dama na tafiya mai nisa musamman don kawai su siya abincin da take siyarwa, duk dai saboda irin diri da take dashi.
Yadda kwastomininta maza ke yaba kyawun jikinta
Da take zantawa da SVTV a shirin Daily Hustle, ta bayyana cewa, wasu mazan na tahowa daga Kasoa, Tema da Gabashin Legon don kawai su siya abincinta.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ta kuma tuna yadda ta fara sana'ar siyar da burodi a baya kafin daga bisani ta sauya zuwa wake da garin rogo bayan samun karin jari.
A cewarta:
"A baya ina siyar da burodi ne sai na yanke shawar kama wannan sana'ar daga inna ta saboda ta tsufa. Don haka ta koya min duk abin da nake bukata daga nan na dauko 'yan kudade na, sai na fara."
Celestina Etornam ta samu damar iya rike kanta
Celestina ta bayyana cewa, wannan kasuwa da take yi ya taimaket ta sosai, inda tace a yanzu ta iya rike kansa.
Daga Aikin Goge-goge Ta Zama Likita: Yar Najeriya Da Tayi Balaguro Zuwa UK Shekaru 10 da Suka Shige Ta Ba Da Labarinta a Bidiyo
Ta ce:
"Ban dogora da kowane namiji ba."
Sai dai, ta ce akwai kalubale da dama game da sana'ar siyar da abinci, amma ta bayyana wadatuwa da abin da take samu da kuma habakar kasuwarta.
Dan Najeriya ya kawo hanyar kawo wutar lantarki da iskar gas daga toroso
A wani labarin kuma, wani matashi ya samo hanyar samar da wutar lantarki ba tare da an sha wahala ba, ta hanyar amfani da masai.
Matashin dan Najeriya ya kera wani nau'in fasaha da ke iya samar da wutar lantarki da kuma iskar gas ta girki.
Jama'a da dama a kafafen sada zumunta sun bayyana mamakin wannan lamari, sun yi martani mai daukar hankali.
Asali: Legit.ng