Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar NNPP Ya Isa Turai Dan Ganawa Da Masana

Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar NNPP Ya Isa Turai Dan Ganawa Da Masana

  • Rabi'u Kwankwaso dai shine jagora kuma dan takarar shugaban kasar a jam'iyyar NNPP a Nigeria
  • Rabi'u Kwankwaso ya fito daga yankin Arewa maso yamma Kukma Shine Dan Takarar Daya Tilo daga Yankin
  • Batun Tuntuba dai da zama wani abu da kowanne dan siyasa ke nema dan goyan baya daga ciki da wajen kasa

Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso dan Takarar Shugaban Kasa na Jam'iyyar NNPP ya isa turai domin gabatar da tuntuba tare neman goyan baya. kamar yadda mai taimakamasa kan kafafen sadarwa ya wallafa a shafin sa na tuwita.

Sanata Kwankwaso ya fara ziyarar ne da kasar Faransa inda ya yi wata ganawa ta musamman da Thomas Gassiloud, wani mai fada aji a Faransa

Ya kuma ziyarci Kwamitin tsaro na Majalisar Dokokin Faransa a birnin Paris, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi moriyar juna tsakanin shugabannin biyu.

Kara karanta wannan

2023: APC Ta Hargitse a Jihar Arewa Yayin da Wani Sanatan Jam'iyyar Ya Gana da Ɗan Takarar PDP

Kwankwaso
Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar NNPP Ya Isa Turai Dan Ganawa Da Masana Hoto: Maitaimakawa Kwankwaso
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ma’aijin Jam’iyyar NNPP Ta Su Kwankwaso Ya Saki Layi, Ya Bayyana Yin Murabus

Ma'ajin jam'iyyar NNPP na kasa, Shehu Ningi, ya bayyana yin murabus daga mukaminsa tare da fita da fitarsa daga jam'iyyar.

Yin murabus din Ningi na iya shafar nasarar Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ta NNPP.

"Ma'ajin NNPP na kasa, Hon Shehu Barau Ningi ya fice daga jam'iyyar, muna fatan ya dawo gidansa na dawo inda a ko yaushe ake masa maraba"

Jam'iyyun siyasa a Najeriya na ci gaba da fuskantar sauya sheka yayin da ake ci gaba da tunkarar babban zaben 2023, shekarar da Manjo Buhari mai ritaya zai sauka a mulki gaba daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida