Kamar Buhari, Tinubu Na Neman Taimakon Kudi Daga Wajen Yan Nigeria
- A kakar yakin neman zaben shekarar 2015 dai shugaba Buhari dai ya nemi taimakon Nigeria da Tallafin kudin kamfe
- Shugaba Buhari dai Shine Dan Siyasar da ya fara neman talakawa su taimaka masa da kudin kamfen bayan dawowa dimukuradiyya tun 1999
- Ana Ganin dai neman taimakon talakawa wata hanya ce da ke nuna cewa dan takarar ko dan siyasar baida kudin yakin neman zabe
Abuja: Jam'iyyar APC mai mulki a Nigeria ta kaddamar da manhajar neman taimakon kamfen din dan takarar shugaban kasa da mataimakin sa Tinubu/Kashim
Jam'iyyar Apc dai ta sanar da hakan ne a shafin ta OfficialAPCNg wanda yake da tabbatcin ingancin mallaka daga kamfanin tuwitta tana mai nuna cewa "kaima zaka iya taimakawa.
Wannan salon dai shugaba Muhammadu Buhari ya fara kaddamar da irinsa, inda yace ko kudin siyan tikitin takara ma bai dashi.
A wancan lokacin dai anyi amfani da katin da aka sarrafa mai dauke da hotan sa da kuma kuma lambobin da za'a danna dan tura masa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
To sai dai a yanzu bayan samun ci gaban fasahar sadarwa, jam'iyyar APC ta fitar da salon taimakawa yakin neman zaben ne ta hanyar amfani da kafar intanet wato ta adireshin https://t.co/QJu2KDNapC
Mai 'Yan Nigeria Ke Cewa
Yan Nigeria dai dama na Tofa Albarkacin bakinsu game da wannan batun ko kuma tsarin da jam'iyya APC ta fitar
@EboDubem yace:
"A tallafawa wa? wai wadanne mutane, shin kuna nufin na bayar da kudi na airin wannan yanayi da ake ciki"
@Kanu
"Haba dai na taimaka musu ace da ni aka tallafa musu su kwashe kudin mu"
Shi kuwa @JccMizzbroze cewa yace
"Wai mai yasa sai kun nemi tallafi?
Wannan Batun dai zai zama dai wani sabon salon siyasa da ba kasafai ke faruwa a nigeria ba musamman ma yadda ake ganin yan takarkarun sun rike mukamai da dama.
Kamar Misali Mataimakin dan Takarar shugaban Kasa, tsohon gwamnan jihar Barno ne, kuma sanata ne mai ci a yanzu.
haka zalika ma Dan takarar shugaban kasa tsohon gwamnan jihar Legas ne kuma shararren dan kasuwa.
Asali: Legit.ng