Ganduje Ya Haramtawa Masu Adaidaita Sahu Bin Wasu Titunan Kano

Ganduje Ya Haramtawa Masu Adaidaita Sahu Bin Wasu Titunan Kano

  • Gwamnatin jihar Kano karkashin shugabancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya hana ‘yan adaidaita bin wasu titunan jihar
  • Titunan da hakan ya shafa sun hada da titin Ahmadu Bello zuwa Mundubawa da na Tal’udu zuwa Gwarzo kamar yadda KAROTA ta sanar
  • Hukumar KAROTA ta kara da cewa, nan gaba kadan za a kara rufewa ‘yan adaidaita wasu titunan bayan an samar da manyan motocin daukar al’umma

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yayi umarnin hana matuka adaidaita sahu bin wasu daga cikin manyan titunan birnin Kano daga ranar Laraba mai zuwa.

Adaidaita Sahu a Kano
Ganduje Ya Haramtawa Masu Adaidaita Sahu Bin Wasu Titunan Kano. Hoto daga aminiyadailytrust.com
Asali: UGC

Jaridar Aminiya ta rahoto cewa, hana bin manyan titunan yana kunshe ne a wata sanarwa da Hukumar Kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano (KAROTA) ta fitar a safiyar Talata ta hannun Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, wanda shi ne kakakin hukumar.

Kara karanta wannan

Da Dumi: Majalisar Osun ta Fatattaki Bukatar Sabon Gwamna na Sauya Sunan jihar

Abinda sanarwar ta kunsa

Channels TV ta rahoto kamar yadda sanarwar ta bayyana:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Gwamnatin jihar ta dauka wannan matakin ne bayan ta samar da titunan da manyan motoci zasu ringa bi suna daukar jama’a a kan titunan da aka hana ‘yan adaidaita bi.”

Sanarwar ta kara da cewa, daga cikin titunan da aka haramtawa adaidaita sahu bi akwai titin Ahmadu Bello zuwa Mundubawa da titin Tal’udu zuwa Gwarzo.

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa, ta tanadar da manyan motocin sufuri don saukakawa jama’a bin wadannan hanyoyin.

Har ila yau, KAROTA ta kara da cewa za a sanar da ranakun da masu tuka adaidaita sahu zasu daina bin karin wasu hanyoyin bayan ta samar da ababen hawa da za a yi amfani dasu a hanyoyin.

Akwai yuwuwar sake haramta bin wasu karin hanyoyin nan gaba kadan bayan samar da isassun ababen hawa da motoci da zasu wadaci al’umma.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotun Daukaka Kara Ta Ayyana Machina Matsayin ‘dan Takarar Yobe ta Arewa

’Yan adaidaita sahu sun fada yajin aiki a Kano

A wani labari na daban, jaridar Legit.ng ta kawo muku cewa matukan babur mai kafafu uku wanda aka fi sani da adaidaita sahu sun fada yajin aiki a ranar 10 ga watan Janairun 2022.

Kungiyar matukan adaidaita sahun ta zargi gwamnati da tatse mambobinta ta hanyar karbar haraji da kuma zuga kudin rijista.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: