Yanzu Yanzu: Kotu ta Aika Shugaban Jam’iyyar APGA, Njoku Magarkama

Yanzu Yanzu: Kotu ta Aika Shugaban Jam’iyyar APGA, Njoku Magarkama

  • Alkalin ya yi umurnin daure masa Shugaban jam'iyyar APGA, Cif Edozie Njoku da wani mutum daya a magarkamar Suleja
  • Ana tuhumar Njoku da Nwoga da kirkirar wata tagardar hukuncin kotun koli na bogi wanda ya mayar da su kujerar shugabancin jam'iyyar
  • Za a ci gaba da tsare su har zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba, lokacin da alkali zai yanke hukunci kan bukatar bayar da belinsu

Abuja - Wata babbar kotun Abuja da ke Bwari ta yi umurnin garkame shugaban jam’iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA), Cif Edozie Njoku da wani a gidan gyara hali.

Ana zarginsu da kasancewa da hannu wajen kirkirar wani hukuncin kotun koli na bogi, jaridar The Nation ta rahoto.

Edozie Njoku
Yanzu Yanzu: Kotu ta Aika Shugaban Jam’iyyar APGA, Njoku Magarkama Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Vanguard ta rahoto cewa hukumomin yan sanda na zargin Njoku da Nwoga da kirkirar wata wasika na kotun koli wanda ya mayar da su a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa da kuma shugaban matasan APGA na kasa.

Kara karanta wannan

Daga Twitter: Matashi ya jefa kansa a matsala, ya shiga hannu bayan zagin Aisha Buhari

Za su ci gaba da zama a magarkama har zuwa zama na gaba

Da yake zartar da hukunci a ranar Litinin, 28 ga watan Nuwamba, mai shari’a Mohammed Magudu, ya yi umurnin tsare Njoku da wani da ake kararsu tare, Chukwuemeka Nwoga a gidan yarin Suleja da ke jihar Neja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma bukaci a ci gaba da tsare su har zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba lokacin da zai zartar da hukunci a kan bukatar bayar da belinsu.

Lauyansu, Panam Ntui ya yi muhawarar neman a bayar da belinsu jim kadan bayan sun ki amsa tuhume-tuhume 14 da ake masu da sunan Sufeto Janar na yan sanda.

Lauyan mai kara, Rimamsomte Ezekiel, ya yi adawa da bukatar neman belin, yana mai cewa laifukan da ake tuhumar wadanda ake kara ba karami bane.

A cewar Ezekiel wasu daga cikin tuhume-tuhumen da ake masu suna dauke da hukuncin akalla daurin shekaru 14 a gidan yari.

Kara karanta wannan

Atiku: Zan Fitar Da Sunayen Ɓarayin Man Fetur, Zan Kunyata Su Idan An Zabe Ni Shugaban Ƙasa A 2023

Aisha Binani ta koma Yola bayan nasarar da ta samu a kotun daukaka kara

A wani labari na daban, mun ji cewa dandazon jama'a sun tarbi Aisha Binani a filin jirgin sama na Yola don yi mata maraba da dawowa mahaifarta daga Abuja.

Wannan ne karo na farko da yar takarar gwamnan na APC a jihar Adamawa ke komawa jihar tun bayan da tayi nasara kan Nuhu Ribadu a kotun daukaka kara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng