Abdulsamad Rabiu Zai Karbi Ragamar Dangote Ta Wanda Ya Fi Kowa Kudi a Afrika, Yana Samun N3.4bn a Kullum
- Tseren attajiran Najeriya na ci gaba da bunkasa yayin da attajiri Abdulsamad Rabiu ke kara matsowa ga matsayin Dangote
- A yanzu haka, Abdulsamad ne attajiri na biyu mafi kudi a Najeriya duk da kuwa a 'yan shekaru ukun nan ya fara bunkasa
- Dangote ne dan kasuwa kuma attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika, amma a yanzu Abdulsamad na samun N3.4bn kullum
Abdulsamad Rabiu a yanzu ya zama na biyu a jerin attajiran da suka fi kowa kudi a Najeriya, kuma yana kusantar matakin Dangote.
Bayanai daga jadawalin Forbes na attajirai ya nuna cewa, ya zuwa ranar Litinin 28 ga watan Nuwamba, Abdulsamad na da $7bn, babban karin da ya samu daga $4.4bn da ya mallaka a farkon 2022.
Wannan na nufin cewa, attajirin dan kasuwan dan jihar Kano ya samu karin $2.6bn (N1.15tr) a cikin watanni 11 kacal.
Abdulsamad na kusantar matakin Dangote
Bal ma, idan aka raba abin da Abdulsamad ya samu cikin kwanaki 331 na shekarar 2022, a kullum yana samun kimanin N3.42bn.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Forbes ta nuna Abdulsamad a matsayin na 318 a jerin attajiran duniya, kenan ya tashi daga na 719 da yake a Janairun 2022.
Tashin arzikin Dangote a 2022
A karon farko, Dangote ya samu kishiya a fannin kasuwanci da kuma matsayi a jerin attajirai a Najeriya. Dangote ne attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika duk da kuwa Abdulsamad ya fara bunkasa ainun.
A cewar Forbes, Dangote ya samu $1.3bn a 2022, inda dukiyarsa ta koma $12.9bn ya zuwa ranar Litinin daga $11.6bn na farkon shekarar nan.
Wannan na nuna cewa, gibin arzikin Dangote da Abdulsamad bai wuce $5.9bn ba idan aka kwatanta da $8.5bn na farkon 2022.
Raguwar arzikin Mike Adenuga
A bangarensa, 2022 ba shekarar shagali bace ga Mike Adenuga, wanda ya samu raguwar dukiya zuwa $5.6bn idan aka kwatanta da $6.6bn a Janairun 2022.
Raguwar dukiyarsa ke nuna ficewarsa daga matsayin na biyu a jerin attajiran Najeriya.
A yanzu shine mutum na 427 a jerin attajiran duniya.
Duk da haka, Dangote ya bange mutane da yawa a jerin attajiran duniya a shekarar 2022 duba da irin ribar da ya girba a cikin watanni kadan.
Asali: Legit.ng