Gagarumar Gobara ta Tashi a Fitacciyar Kasuwa Onitsha, Ana Kokarin Kashewa
- Gagarumar gobara ta tashi a fitacciyar kasuwar Onitsha dake jihar Anambra da tsabar daren Litinin 28 ga watan Nuwamban 2022
- Wani ‘dan kasuwa mai suna Obenta Jude ya bayyana cewa har yanzu jami’an kashe gobara suna ta kokarin kashe wutar a kasuwa
- Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Anambra, Martin Agbili, yace sun samu kiran gaggawa kuma sun tura jami’ai da gaggawa
Onitsha, Anambra - Wani sashi na fitacciyar babbar kasuwar Onitsha dake jihar Anambra ya kone, jaridar The Nation ta rahoto.
Abinda ya assasa gobarar da ta fara wurin tsakiyar dare har yanzu ba a tabbatar ba.
Wani ‘dan kasuwa dake da shago a kasuwar mai suna Obenta Jude yace rukunin shaguna biyu ne suka kone a titin Kano a sakamakon gobarar.
Yace duk kokarin da jami’an hukumar kashe gobara suka yi wurin kashe mummunar gobarar ya tashi a banza saboda gobarar ta cigaba da ci babu kakkautawa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A yayin tabbatar da faruwar lamarin, shugaban hukumar kwana-kwana, Injiniya Martin Agbili yace jami’an hukumar sun hanzarta zuwa wurin bayan an sanar musu abinda ke faruwa.
Yace:
“Wurin karfe 2:20 na daren Litinin, 28 ga watan Nuwamban 2022 ne hukumar kashe gobara ta jihar Anambra ta samu kiran gaggawa kan cewa gobara ta tashi a titin Kano dake babbar kasuwar Onitsha.
“Sai dai, mun hanzarta tura motar kashe gobara da ma’aikata zuwa wurin kuma suna ta aiki a kai. Sun je cika motar da ruwa har sau biyu.”
’Yan Sanda sun yi martani
A yayin martani kan lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace yanzu haka an shawo kan lamarin kuma babu rai da aka rasa duk da kayan miliyoyin naira sun kurmushe.
Ya bayyana cewa, binciken farko da aka gudanar an gano cewa wutar ta fara ne sakamakon wutar lantarki da ta kama a wani shagon siyar da kayan kwalliya dake wani bene.
Ikenga yace ‘yan sandan dake lura da wurin har yanzu suna inda ake gobarar domin tabbatar da tsaron kayayyaki.
Kakakin rundunar ‘yan sandan kamar yadda jaridar Channels TV ta rahoto, yayi amfani da damar wurin kira ga jama’a da su dinga kashe kayayyakin wutar lantarkinsu kafin su bar Ofisoshi sun da gidajensu.
’Yan daba sun kone ofishin INEC a Ebonyi
A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto muku yadda wasu da ba a san ko su waye ba suka kurmushe ofishin hukumar INEC da Izzi a Ebonyi.
Hukumar zaben mai zaman kanta ta tabbatar da cewa sun tafka muguwar barna.
Asali: Legit.ng