Jihar Kano Za Ta Fara Kera Gwala-Gwalai a Shekarar 2023, Gwamnatin Buhari
- Gwamnatin tarayya ta bayana cewa kasar Najeriya zata fara kera gwala-gwalai a 2023
- Kamar yadda FG ta sanar, tuni aka fara horar da yan Najeriya kan yadda zasu kera dankunnaye, awarwaro da sauran kayan ado na gwal
- Wannan kasuwa ta gwala-gwalai zata kasance a jihar Kano kuma zata yi gogayya da takwarorinta na duniya
Abuja - Ma’aikatar ma’adinai da karafa, ta bayyana cewa kasuwar gwala-gwalai ta jihar Kano da sauran ayyuakan da take aiwatarwa zai fara aiki daga 2023, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Ministan ma’adinai, Mista Olamilekan Adegbite, ne ya fadi haka yayin da ya ke zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Abuja.
Adegbite ya ce kasuwar gwala-gwalan za ta kasar ta zama cibiyar gwala-gwalai ta duniya.
An fara horar da wadanda za su yi aikin kera gwala-gwalan
Kaddara Ta Riga Fata: Kyakkyawar Budurwa Ta Kaso Aurenta Bayan Watanni 3, Ta Wallafa Hotunan Shagalin Bikin, Jama’a Sun Yi Martani
Ya ce gwamnati ta horar da mutanen da za su dunga kera gwala-gwalai, yana mai cewa za su kasance mazauna a wannan kasuwar ta gwala-gwalan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“A Kano, Ana fitar da gwala-gwalanmu daga Najeriya zuwa kasashe kamar Dubai da sauransu inda suke nakar da su zuwa kayan ado.
“Kuna siyansu da farashi mai tsada amma a lokacin da wadannan gwala-gwalan ke barin Najeriya a danyensu, sun siyansu ne kusan kamar kyauta.
“Don haka, muka ce bari mu samu kasuwar kera gwala-gwalai wanda zai yi gogayya da kowace kasuwar gwal a duniya.
“Za su narkar da gwala-gwalai a Najeriya su zama kayan ado. Za su iya yin awarwaro, dankunnaye, sarkoki da sauransu.
“An horar da mutane don yin wannan a yanzu. Don haka, muna kara fito da darajar Najeriya kuma muna cewa kasuwar gwala-gwalan Kano zai iya shiga rukunin kasuwanni gwala-gwalai na duniya.
“Wannan zai ba mutane damar sanin cewa wani lokaci na shekara, za mu shirya bikin gwala-gwalai a kasuwan na Kano don mata da zama daga ko’ina na duniya su zo Kano sannan su siya gwal.
“Wannan shine dalilin da yasa muke da dukkanin ayyuka a yankunan nan shida kuma wadannan aiki suna matakin kammaluwa.
“Za mu kaddamar da su nan ba da jimawa ba. Za mu duba lokacin da ya dace don bikin kaddamar da wadannan ayyukan a farkon shekara.”
Asali: Legit.ng