Gwamnatin Buhari ta Bayyana Adadin Kudin da Ta Kwato Daga Mahandama tun Daga 2015
1 - tsawon mintuna
- Gwamnatin Buhari ta sanar da cewa ta samo $1 biliyan na kudaden da mahandama suka wawure a kasar nan tun bayan hawan mulkinsa
- Abubakar Malami, antoni janar na tarayya kuma ministan shari’a na kasar nan ya sanar da hakan ga manema labaran gidan gwamnati a Abuja
- Ya bayyana cewa, an waskar da kudaden zuwa sassan amfani masu yawa a kasar nan da suka hada da tattalin arziki tare da yaki da fatara
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya tace $1 biliyan ta kwato daga kudaden da aka wawure tun bayan hawan mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, jaridar Vanguard ta rahoto.
Abubakar Malami, Antoni janar na tarayya ya bayyana hakan a ranar Laraba.
Yayi wannan jawabin ne a yayin zantawarsa da manema labaran gidan gwamnati bayan taron majalisar zartarwa na tarayya a fadar shugaban kasa dake Abuja, jaridar TheCable ta rahoto.
Kamar yadda malami yace, kudaden da aka samo an yi amfani dasu a sassa da yawa da suka hada da tattalin arziki har da fatattakar fatara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Karin bayani na nan tafe…
Asali: Legit.ng