Jerin Bukatu 5 Da Kungiyar CAN Ta Gabatarwa Atiku Abubakar a Zamansu
- Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana jerin bukatun da shugabannin Kiristocin Najeriya CAN suka basa
- Wannan shine karo na biyu da kungiyar za ta zauna da wani yan takara kujerar shugaban kasa
- A zamanta da dan takarar APC, Asiwaju Bola Tinubu, CAN ta gabatar masa da bukatu bakwai cir
Abuja - Dan takarar kuejrar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP a ranar Talata, 22 ga Nuwamba, ya zanna da shugabannin kungiyar Kiristocin Najeriya a Abuja.
Tsohon mataimakin shugaban kasan tare da abokin tafiyar, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta sun samu rakiyar shugaban uwar jam'iyyar PDP, Dr. Iyorchia Ayu da sauran jigogin jam'iyyar.
Atiku da kansa ya zayyano bukatun da shugabannin na CAN suka yi masa a jawabin da ya fitar a shafinsa na Twitter.
Yace:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Ina Cibiyar Kiristocin Najeriya Abuja domin tattaunawa da kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN)."
"Na kammala zaman tattaunawa da CAN. Na ji dadi sosai saboda manufofina na gyara Najeriya duk daya ne da bukatunsu."
Na godewa kwamitin majalisar zartaswar CAN bisa wannan dama domin yi musu bayanai kan yadda nike son sauya Najeriya. Ina kyautata zaton sake tattaunawa da wasu masu ruwa da tsaki a kasar nan
Ga Jerin bukatun da suka yi masa
1. Yiwa Najeriya garambawul
2. Samar da tsaro
3. Samawa matasa aikin yi
4. Hada kan dukkan kabilu
5. Kawo sauyin rayuwa
Zaman Tinubu da kungiyar CAN
Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu ya yi watsi da jita-jitan cewa yana kokarin Musuluntar da kasar.
Asiwaju ya fadi hakan ne yayin zamansa da shugabanin kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ranar 17 ga Nuwamba, 2022.
Tinubu ya yi musu bayanin cewa ko a gidansa Kiristoci sun fi Musulmai yawa, shi kadai ne Musulmi.
A cewarsa, idan ya gaza Musuluntar da matarsa da 'yayansa, ta yaya zai Musuluntar da kasa irin Najeriya.
Yace:
"Jita-jitan da ake yadawa cewa ina shirin mayar da Kiristocin Najeriya saniyar ware ba gaskiya bane kuma da ban takaici. Bani da wata manufar yin hakan."
"Zaune da ni a nan uwargidata ce... Ban isa in yi takarar zabe a cikin gidana ba sbaoda zan sha kashi. Sukkansu na zuwa Coci ranar Lahadi su bar ni a gida."
Asali: Legit.ng