Minista Sadiya Ta Tuhumci Ministar Kudi Da Cusa N206bn Cikin Kasafin Kudin 2023
- Karo na uku, an tuhumci ministar kudi da cusa kudaden boye cikin kasafin kudin Najeriya 2023
- Majalisar dattawa ta ce a sammaci Ministar kudi, Hajiya Zainan Ahmed Shamsuna, cikin gaggawa
- Gwamnatin tarayya na karban basussuka tiriliyoyi don aiwatar da ayyukan kasafin kudin 2023
Abuja - Ministar Tallafi da jin dadin al'umma, Sadiya Farouq, ta tuhumci Ministar Kudi, Zainab Ahmed, da sanya kudi N206bn cikin kasafin kudin ma'aikatar na 2023.
Hajiya Sadiya ta bayyana hakan ne ga kwamitin majalisar dattawa ranar Litinin inda ta tafi munakasha kan kasafin kudin ma'aikata na 2023, rahoton Punch.
Tace akwai wasu kudade na hukumar cigaban yankin Arewa maso yamma da aka sanya a kasafin kudin 2022 amma ba'a basu kudaden ba, yanzu kuma an sake sanya kudin cikin na 2023 har ninkin ba niki.
An fara takkadama ne lokacin Sanata Elisha Abbo (APC Adamawa North), ya tuhumci Sadiya da cusa kudi N206bn cikin kasafin kudi, riwayar AIT.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Minista Sadiya tace:
"Ba'a bamu kudaden ba, yanzu kuma muna ganin ya ninku kusan ninki 10, zamu tambayi ma'aikatar kudi tayi mana bayani kan dalilin sanya kudin ciki duk da cewa ba'a fitar ba a bara."
Jawabin Sanatoci
Sanata Abbo ya bayyana mamakinsa bisa jawabin Ministar.
Ya ce ta wani dalili za'a rika karban basussukan kudade da sunan ana amfani dasu wajen aiki alhalin ba'a amfani da su.
Yace:
"Wannan babban lamari ne. Ba zamu iya cigaba da karban basussuka ba kuma babu wani abin kirki da za'a ga an yi da kudin ba."
Shugaban kwamitin, Sanata Yusuf Yusuf ya bukaci a sammaci Ministar kudi tayi bayanin yadda ta cusa N206bn cikin kasafin kudin 2023.
Wannan ba shine bane karon farko
Wannan ba shine karon farko da za'a tuhumci Ministar kudi da cusa kudaden boye cikin kasafin kudin ba.
A ranar Alhamis, ministan tsaro ya bayyanawa majalisar dattawa cewa Minista Zainab ta cusa N11bn cikin kasafin kudi ma'aikatarsa, hakazalika Ministan lafiya ba haka.
Yadda aka kashe N2tr ta bayan fage, Majalisa ta Bada Shawarar a Rusa Wasu Ma’aikatu
Kwamiti da aka kafa domin binciken ayyukan ma’ikatun gwamnatin tarayya ya yi bayanin yadda akayi rub da ciki kud N2tr.
Majalisar ya bada shawarar rusa wasu hukumomin kasar.
Asali: Legit.ng