Gwamnan Gombe Ya Nada Yakubu Kwairanga a Matsayin Sabon Sarkin Funakaye

Gwamnan Gombe Ya Nada Yakubu Kwairanga a Matsayin Sabon Sarkin Funakaye

  • Masarautar Funakaye da ke jihar Gombe ta samu sabon sarki watanni bayan mutuwar tsohon sarki, Muazu Muhammad Kwairanga III
  • Gwamna Inuwa Yahaya ya nada Alhaji Yakubu Muhammad Kwairanga a domin ya shugabanci masarautar a matsayin sabon sarki
  • Kwamishinan harkokin sarauta, Alhaji Ibrahim Dasuki Jalo ne ya sanar da hakan a yau Litinin, 21 ga watan Nuwamba

Gombe - Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya amince a nada Alhaji Yakubu Muhammad Kwairanga a matsayin sabon sarkin Funakaye.

Nadin nasa na kunshe ne a cikin wata wasika dauke da sa hannun kwamishinan da ke kula da harkokin masaraitu, Alhaji Ibrahim Dasuki Jalo an kuma gabatar da shi ga manema labarai a Gombe a ranar Litinin, jaridar Vanguard ta rahoto.

An nada sabon sarkin Funakaye
Gwamnan Gombe Ya Nada Yakubu Kwairanga a Matsayin Sabon Sarkin Funakaye Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Kamar yadda kwamishinan ya bayyana, nadin ya yi daidai da ikon da gwamnan ke da shi karkashin Dokar Masarautun Jihar Gombe ta 2022 da kuma shawarwarin masu nada sarki na masarautar Funakaye da kuma tuntuba.

Kara karanta wannan

Sojin sama sun kassara karfin Turji, sun yi kaca-kaca da maboyar mai kawo masa makamai

Yakubu Kwairaga ya gaji marigayi Sarki Muazu Muhammad Kwairanga III

Yayin da yake gabatar da wasikar nadin ga sabon sarki a fadar sarki da ke Bajoga, karamar hukumar Funakaye, Hon Dasuki, ya bukaci basaraken da ya gina kyakkyawar alaka a masarautarsa sannan ya dora daga inda magabatansa suka tsaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Allah madaukakin sarki ya zabi Yakubu Muhammad Kwairanga a matsayin sarkin wannan masarauta na gaba daga cikin yan takara da daman a gidan sarauta, don haka ina rokon daukacin al’ummar Funakaye da su marawa sabon sarki baya.”

Ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin Inuwa Yahaya zata ci gaba da nutunta majalisar sarakunan gargajiya duba ga rawar ganin da take takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Da yake yiwa sabon sarkin fatan shugabanci mai cike da zaman ladiya, kwamishinan ya ce za a yi bikin nadi da gabatar da sandar girims ga sabon sarkin nan gaba, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Majalissar Dattijai Omo Ovie-Agege Yace Shine Ya Dakatar da Kudirin Tsige Shugaba Buhari

Sabon sarkin ka kasance kani ga marigayi Sarki Muazu Muhammad Kwairanga III wanda ya rasu a ranar 27 ga watan Agustan 2022.

Idan za ku tuna, marigayi sarkin ya rasu ne a cikin barcinsa kamar yadda majiyoyi daga masarautar suka bayyana.

Gani na karshe da aka yiwa sarkin ya kasance a taron rabon kayayyakin abinci ga marasa galihu da ministan sadarwa, Dr Isa Ali Pantami ya yi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel