A Boye Matata Ta Kara Auren Wani Daban, Miji Ya Gaya Wa Kotu a Abuja
- Wani magidanci mai suna Victor Ora, ya nuna gajiya wa a aurensa, ya kai ƙarar matarsa gaban Kotu kan zargin ta kara aure
- Mista Victor, ya faɗa wa Kotun Kistumare dake Jikwoyi a birnin Abuja cewa matarsa ta kama gabanta ba tare da izininsa ba
- Bayan sauraron bayanan mai ƙara, Alkalin Kotun mai shari'a Labaran Gusau ya ɗage zama zuwa karshen watan Nuwamba
Abuja - Wani ɗan kasuwa, Mista Victor Ora, ya kai ƙarar matarsa mai suna Comfort gaban Kotun Kostumare dake Jikwoyi, birnin tarayya bisa zargin ƙara aure a ɓoye.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa da yake shigar da ƙara a Kotu, Victor ya bayyana cewa matarsa ta bar gidan aurenta ba tare da izininsa ba.
"Matata ta gudu ta bar gida ba da izini na ba, dana nemota sai take gaya mun wai ta yi aure da wani mutum daban."
"Sabida wannan abu data aikata mun ne nake son a datse igiyoyin auren da ke tsakaninmu," inji Victor.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sun hana ni gadin ɗana
Bayan haka ya faɗa wa Kotun cewa 'yar uwar matarsa ta hana shi haɗuwa da ɗansa da suka haifa a zaman auren.
Ya ci gaba da cewa:
"Na samu labarin ɗana na tare da yar uwar matata, sai na je domin na gansa amma abin mamaki ta hana ni haɗuwa da ɗana. Ta rantse cewa zan ganshi ne kawai idan babu rai a jikinta."
"Ina rokon wannan Kotu ta raba wannan auren kuma ta bani damar kula da ɗaukar nauyin ɗana."
Bayan jin ta bakinsa, Alkalin Kotun mai shatri'a Labaran Gusau, ya sanar da ɗage zaman zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba domin a dawo a ci gaba da tafka muhawa kan shari'ar.
Kano: A Zaman Kotu, An Gano Dalilin da Yasa Ɗan China Ya Ba Ummita Kyautar Miliyan N18m da Sabon Gida
An Gano Dalilin Da Yasa Dan China Ya Kashe Wa Ummita Miliyoyi
A wani labarin kuma Ɗan sandan bincike ya bayyana wa Kotun yadda Ɗan China ya kashewa Ummita sama da Miliyan N20m
A ci gaba da sauraron shari'ar kisan Ummita, ɓangaren gwamnatin jihar Kano karkashin kwamishinan Shari'a, Barista Musa Lawan Abdullahi, sun gabatar da ɗan sanda a matsayin shaida ta 5.
Insifekta Injuptil Mbambu ya faɗa wa Alkali cewa a bincikensu sun gano cewa Ɗan China ya ba Ummita kudi ta kama sana'a ya kuma ya saya mata gida.
Asali: Legit.ng