Wani Mutumi Ya Jibgi Matarsa Har Ta Mutu Saboda Ta Hana Shi Kadararta a Ogun

Wani Mutumi Ya Jibgi Matarsa Har Ta Mutu Saboda Ta Hana Shi Kadararta a Ogun

  • 'Yan sanda sun cafke wani magidanci, Ebenezer, bisa zargin lakaɗa wa matarsa duka har ta mutu a jihar Ogun
  • Bayanai sun nuna cewa mutumin ya buga wa matar Kwaɗon karfe yayin da yake bugunta kan wani saɓani da ya haɗa su
  • Mai magana da yawun 'yan sandan Ogun yace kwamishina ya ba da umarnin tsananta binci da ɗaukar mataki

Ogun - Rudunar yan sandan jihar Ogun ta damƙe wani magidanci ɗan shekara 45, Segun Omotosho Ebenezer, bisa zargin jibgar matarsa, Omotosho Olubukola, har tace ga garinku nan.

Jaridar Daily Trust tace wanda ake zargin ya shiga hannu ne a maɓoyarsa ƙauyen Akinseku, Abeokuta, babban birnin jihar Ranar Lahadi.

Hukumar yan sanda.
Wani Mutumi Ya Jibgi Matarsa Har Ta Mutu Saboda Ta Hana Shi Kadararta a Ogun Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Bayanai sun nuna cewa mutumin ya narka wa matar Kwado na ƙarfe a kai kuma ya ji mata munanan raunuka a ilahirin jikinta.

Kara karanta wannan

Ana Tsaka da Shan Soyayya, Budurwa Ta Burma Wa Saurayinta Sadiq Ɗahiru Wuka Har Lahira

An tattaro cewa wanda ake zargin, mai sana'ar Kafinta ya samu saɓani da mai ɗakinsa ne saboda ta ƙi yarda ta damƙa masa ragamar makarantar kuɗin da ta gina.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wane saɓani ne ya haɗa su?

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da kama wanda ake zargin ranar Litinin. Yace yar uwar matar ta faɗa musu cewa Ebenezee ya ji wa matar raunuka kan karamin saɓani.

Wanda ake zargi da kansa ya garzaya da matar babban Asibitin tarayya FMC Idi-Aba Abeokuta domin kula da ita amma rai ya yi halinsa.

"Mijin bai sani ba, marigayyar ta tura sakon murya ga yan uwanta ta gaya nusu cewa Mijinta ya buga mata Kwaɗo a kai yayin da yake jibgarta, idan ta mutu su sani shi ne ya kasheta."

Kara karanta wannan

Kano: A Zaman Kotu, An Gano Dalilin da Yasa Ɗan China Ya Ba Ummita Kyautar Miliyan N18m da Sabon Gida

"Bayan jin sakon muryar, Magidancin ya gudu amma bayan samun rahoto DPO na caji Ofis ɗin Kemta ya umarci jami'ai su nemo mutumin duk inda ya shiga. Bincike ya nuna sun samu saɓani ne kan wata makaranta."
"Marigayyar ta gina makarantar da sunanta da mijin amma Magidancin ya nemi ya karɓe makarantar baki ɗaya ita kuma ta ƙi yarda, asalin sabanin da ya ja kullum yake jibgarta har wannan rana ta zo."

- Mista Oyeyemi.

Ya ƙara da cewa kwamishina ya umarci a maida wanda ake zargi bangaren kisan kai na sashin binciken aikata manyan laifuka domin tsananta bincike da ɗaukar mataki, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A wani labarin kuma Yan sanda sun damƙe wata Budurwa kan zargin halaka Saurayinta a jihar Legas

Rahoton ya nuna cewa matashiyar mai suna Esther Paul, yar shekara 27 a duniya ta burma wa saurayinta wuƙa har rai ya yi halinsa a Layin Oba Amusa, Lekki.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Abubakar Na Shirin Janyewa Daga Takarara Shugaban Ƙasa? Gaskiya Ta Fito

Yan sanda sun gano wuƙar da Eather ta yi amfani da ita wurin aikata wannan ɗanyen aiki, sun ci gaba da bincike kan lamarin kafin zuwa Kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262