NDLEA ta Damke Dattijuwa mai Takaba Dauke da Hodar Iblis a Takalman Kafarta Zata Kai su Saudiyya
- Jami’an NDLEA sun cafke wata mata mai takaba dauke da 400grams na hodar iblis da ta boye a cikin takalman da take sanye dasu a kafarta
- Matar mai suna Ajisegiri Kehinde Sidika mai shekaru 56 tayi ikirarin ita ‘yar kasuwa ce kuma tana kan hanyarta ne na zuwa kasar Saudi Arabia
- Jami’an hukumar NDLEA din sun lura da takalman dake kafarta inda suka titsiyeta tare da bare su sannan aka gano muguwar kwayar
Legas - Jami’an hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA sun damke wata tsohuwa mai takaba mai shekaru 56 kuma mahaifiyar yara hudu a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad dake Ikeja a jihar Legas kan yunkurin safarar hodar iblis mai nauyin 400grams boye a takalma zuwa Saudi Arabia.
Wacce ake zargin tayi ikirarin cewa ita ‘yar kasuwa ce dake siyar da kayan manya da yara a Legas kuma an kama ta a ranar Lahadi, 13 ga watan Nuwamban 2022 yayin da take kokarin hawa jirgin Qatar Airways zuwa Saudi Arabia inda zasu biya ta Doha.
Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, a wallafar da yayi a shafin hukumar na Twitter, yace bayan natsuwa da aka yi aka duba takalman da take sanye dasu, an samo sunkin hodar Iblis biyu masu nauyin 400grams.
An kama mai siyar da sassan adaidaita sahu
Har ila yau, yunkurin wani mai siyar da sassan adaidaita Sahu, Ayoade Kehinde Tayo na aikawa da 1kg na Tramadol 225mg da Rohyphnol zuwa Istanbul, Turkiyya ta Cairo a jirgin Misra duk a rana daya an bankado shi tare da kama shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hukumar NDLEA din tace ya je filin jirgin saman don mika boyayyun kwayoyin a jikin jakar kayan abinci ga wani fasinja mai Suna Idowu Ayoade, an kama shi kafin yayi nasarar aiwatar da mugun nufinsa.
NDLEA ta kama mai tsohon ciki da miyagun kwayoyi
A wani labar ba daban, hukumar NDLEA ta kama wata mata mai suna Haruna Favour mai tsohon ciki dauke da miyagun kwayoyi.
Matar mai shekaru 25 ‘yar asalin garin Auchi na jihar Edo ta shiga hannu inda aka kama ta da nau’ikan magunguna na ruwa masu dauke da codeine da sauransu.
Asali: Legit.ng