Kwara: An yi Caraf da Mai Garkuwa da Mutane Yana Tsaka da Siyan Abinci
- ‘Yan sanda sun damke wani da ake zargi da garkuwa da mutane mai suna Umaru mai shekaru 20 yayin da yaje siyan abinci da silifas
- An gano cewa, sun hada baki da wasu inda suka sace yaran wani mutum kuma suka karba kudin fansa wanda aka kama matashi Umaru dasu
- An samu N52,000 a jikinsa wanda bayan binciken ‘yan sanda ya sanar da cewa suna daga cikin kasonsa na kudin fansar da suka karba
Kwara - Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta gurfanar da wani da ake zargi da garkuwa da mutane mai suna Umaru mai shekaru 20, wanda aka kama yayin da yake siyan abinci da silifas a Oro dake karamar hukumar Irepodun.
An gurfanar da shi kan zargin aikata laifuka biyu da suka hada da hada kai wurin aikata laifi da kuma garkuwa da mutane, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Yadda lamarin ya faru
Kamar yadda rahoton farko ya bayyana, wani Ibrahim Umar ya kai korafin cewa yaransa biyu maza, Umaru Ibrahim mai shekaru 14 da Yusuf Ibrahim, mai shekaru hudu, wani Mohammed da wasu mutum biyu masu suna Babangida da Laagi sun yi garkuwa dasu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shafin LIB ya rahoto cewa, ’dan sanda mai gurfanarwar Gbenga Ayeni, ya sanar da kotun cewa:
“Daga bisani sun bukaci kudin fansa da ya kai N30 miliyan amma an biya su N400,000 bayan sasanci. Sai dai, an kama wanda ake zargin daga bisani a Oro inda ya je siyan abinci da silifas.
“An samu N52,000 a jikinsa daga cikin kasonsa na kudin fansar da ya karba bayan an caje shi wanda da kanshi ya bayyana hakan yayin bincike.”
Alkalin kotun majistaren mai suna Isah ya aike wanda ake zargi gidan yari tare da dage sauraron shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Nuwamban 2022.
Soji sun halaka mashahurin ’dan bindiga Kachalla Gudau
Legit.ng ta rahoto mu cewa, sojojin Najeriya sun ragargaza kwamandan ‘yan bindiga a jihar Kaduna mai suna Kachalla Gudau da ya addabi yankunan jihar.
An gano cewa gogaggen ‘dan bindiga ne da ya kware a safarar miyagun kwayoyi, satar shanu da kuma dillancin makamai.
A cikin watanni 6 kacal ya sace shanu 6532 a yankin Kajuru dake jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng