Sauya Fasalin Naira: Miyetti Allah Ta Roki Gwamna CBN Ya Kara Wa'adi
- Kungiyar Miyetti Allah ta roki babban bankin Najeriya CBN ya kara wa'adin daina amfani tsaffin takardun Naira
- Kungiyar ta bayyana cewa idan aka daina karban kudin ranar 31 ga Junairu 2023, mambobinsu da dama za suyi asara
- Sun bukaci gwamnan bankin CBN ya kara wa'adin amfani da kudin da watanni uku don wasu dalilai
Awka - Kungiyar Makiyaya Dabbobi a Najeriya Watau Miyetti Allah (MACBAN) ta bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tsawaita ranar kai tsaffin kudi banki da akalla watanni uku.
Shugaban kungiyar na yankin kudu maso gabas, Alhaji Gidado Siddiki, ya bayyana hakan ne a hirar da ya gabatar da Awka, babbar birnin jihar Anambra ranar Alhamis, 17 ga Nuwamba, 2022, rahoton Punch.
Legit.ng Hausa a baya ta kawo muku labarin cewa babban bankin a ranar 26 ga Oktoba ya sanar da sauya fasalin takardun Naira na N200, N500 da N1,000.
Za'a fito da wadannan sabbin kudi ne ranar 15 ga Disamba, 2022 kuma a daina karbar tsaffin ranar 31 ga Junairu, 2023.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Miyetti Allah ta bayyana dalilanta
Shugaban MACBAN yace sun bukaci karin wa'adin ne saboda mambobinsu dake Karkara da cikin Daji sakamakon irin rayuwar da suke basu da labarin halin da ake ciki, riwayar Independent Newspaper.
Saboda haka a basu daman fitowa bude asusun banki saboda kada suyi asarar kudadensu.
Ya kara da cewa lokacin da irin haka ya faru a shekarar 1985, mambobinsu da dama sun tafka asara.
Yace:
"Muna rokon gwamnati saboda lokacin da irin haka a faru a 1985, mambobinmu da dama dake kiwo a cikin daji sun tafka asara saboda basu samu labari da wuri ba."
"Makonni biyu da aka bada lokacin basu isa makiyaya kai kudadensu banki ba, kuma mafi akasari basu ajiye kudi a banki. Gida suke ajiya."
"Ba zamu iya yaki da gwamnati ba da dokokinta ba; muna rokon CBN ne ta taimaka mana a tsawaita ranakun da watanni 3 don baiwa Miyetti Allah daman kai labari da mambobinta dake wuraren ko layukan sadarwa babu."
Ku Kawo Kudadenku kan su zama banza: Jerin Bankunan Da Suka Kara Ranakun Aiki
A wani labarin kuwa, Biyayya ga umurnin babban bankin Najeriya CBN na tattara kudaden Naira dake yawo cikin jama'a, bankuna sun fara sauya lokutan aikinsu don mutane su samu damar kai kudadensu.
Asali: Legit.ng