Ba Zan Iya Saka 'Skirt' Ko Na Zo Kusa Da Namiji Ba, Inji Wata Budurwar Da Aka Nada Sarauta

Ba Zan Iya Saka 'Skirt' Ko Na Zo Kusa Da Namiji Ba, Inji Wata Budurwar Da Aka Nada Sarauta

  • Wata kyakkyawar matashiya yar Najeriya ta je dandalin TikTok don fadama mutane abubuwan da aka hana ta yi bisa al’ada bayan bata kambun sarauta
  • A cewarta, a kullun ana tsammanin ganinta cikin shiga irin ta maza domin ana mata kallon namiji a al’adance
  • Mutane sun sha mamaki bayan sun ji cewa sarauniyar ba zata yi soyayya ba saboda matsayinta

Wata kyakkyawar budurwa mai suna @callmeregent, wacce ta zama sarauniya ta wallafa wani bidiyo don sanar da mutane abubuwan da aka haramta mata yinsu.

Ta bayyana cewa tun bayan da ta hau wannan kambu na sarauta, bata sanya kyawawan tufafinta na mata. A cewarta, an haramta mata sanya su a al’adance.

Sarauniya
Ba Zan Iya Saka 'Skirt' Ko Na Zo Kusa Da Namiji Ba, Inji Wata Budurwar Da Aka Nada Sarauta Hoto: TikTok/@callmeregent
Asali: UGC

Abubuwan da al’ada ya haramtawa sarauniya

A bidiyon da ta wallafa, an gano ta cikin cikakkiyar shiga irin ta gidan sarauta yayin da hannaye da wuyanta ke dauke da duwatsun ado irin da saraki.

Kara karanta wannan

Kyakkyawa Ce: Bidiyon Dirarriyar Amarya Mai Ji Da Tsawo Sanye da Takalma Masu Tsini a Ran Aurenta Ya Ja Hankali

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mafi girma daga cikin abubuwan da aka haramta mata yi shine kusantar namiji saboda al’ada na yi mata kallon namiji ce ita ma. Hakazalika an haramta mata cin abinci a waje.

Kalli bidiyonta a kasa:

Jama’a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:

user1396829741646 ya ce:

“Menene dalilin da yasa ba zaki kusanci namiji ba, gara ma ki ajiye masu abunsu, idan da nice da zan fara tambayansu ko nayi masu laifi ne.”

Ifelewa ta ce:

"Ahahha, shin baki yi kankata da wannan ba..ban san har yanzu irin wannan na faruwa ba.”

Kofomi ya ce:

“Ya batun saurayinki fa”

Ga kyau ga tsawo: Bidiyon wata kyakkyawar amarya mai tsawo ya dauka hankali

Wata kyakkyawar amarya mai ji da tsawo da diri ta ja hankalin jama'a a soshiyal midiya bayan ta bayyana shiga ta kasaita a wajen liyafar bikinta.

Kara karanta wannan

Bidiyon Matashi Sanye da Atamfa, Jakarsa, Agogo da Motarsa duk Tsarin Atamfar

Abun da ya fi daukar hankali game da ita shine yanna ta sanya takalma masu tsini duk da baiwar tsawo da Allah ya yi mata sannan ta shashe abunta a kansu.

Hakazalika, duk jama'ar da suka kewayeta sai suka zamo wasu gajajjeru domin duk tana iya kallon har cikin tsakiyar kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng