Ku Kawo Kudadenku: Jerin Bankunan Da Suka Kara Ranakun Aiki Don Sauyin Fasalin Naira
- Wasu bankunan Najeriya sun sanar da sauye-sauyen na lokutan aikinsu don karban kudaden yan Najeriya kafin wa'adin gwamnati ya shude
- Bankuna da sun aikawa kwastamominsu sakonni sanar da su cewa za'a fara bude bankuna ranar Asabar
- A ranar 15 ga watan Disamba, babban bankin Najeriya CBN ta ce za'a saki sabbin kudaden N200, N500, N1000
Biyayya ga umurnin babban bankin Najeriya CBN na tattara kudaden Naira dake yawo cikin jama'a, bankuna sun fara sauya lokutan aikinsu don mutane su samu damar kai kudadensu.
A sakon akwatin email da suka aikawa kwastamominsu, bankunan sun bayyana cewa sun sauya ranakun aikinsu ne don taimkawa kwastomomi wajen zuba kudadensu a banki kan ranar 31 ga Junairu da CBN ya bada wa'adi.
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa akalla N2.73 Trillion na kudaden Naira dake yawo cikin jama'a zasu dawo banki idan aka sauya fasalin N200, N500, da N1000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga jerin Bankunan da sakonnin da suka aike
Access Bank tace:
"Zamu tsawaita lokutan aikinmu na mako, sannan kuma zamu fara bude ranar Asabar daga karfe 10 am zuwa 2pm don karban kudade."
Tace:
"Yanzu zaku iya kawo tsaffin kudadenku kafin ranar 31 ga Junairu, 2022 da akayi wa'adi. Zamu bude karfe 10 zuwa karfe 3."
UBA
Bankin United Bank for Africa (UBA) shima ya ce za'a fara budewa ranar Asabar, rahoton TheCable.
Bankin yace zai bude Asaba daga karfe 10 na safe zuwa 2 na rana.
"Sakamakon sanarwar CBN na sauya fasalin Naira, zamu zamu fara budewa ranar Asabar daga karfe 10:00 na safe zuwa 2:00 don karban kudade kadai."
Saura bankuna ma sun aika ire-iren wadannan sakonni ga kwastamominsu.
Majalisa ta amince a sake fasalin Naira, amma ta tono wani batu mai girma
Majalisar dattijai a ranar Laraba ta bayyana amincewarta ga shirinbabban Najeriya (CBN) na sake fasalin kudin Najeriya, The Nation ta ruwaito
Amma ta yi tsokaci da cewa, karshen watan Janairu ya yi kusa ga mayar da kudaden da ke yawo a kasar zuwa banki.
Shugaban kwamiti harkokin banki, inshora da hada-hadar kudi, Sanata Sani Uba ne ya bayyana haka.
Asali: Legit.ng