Ba Za a Biya Ku Albashin Aikin Da Baku Yi Ba – FG Ga Malaman ASUU
- Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dage kan bakarta na kin biyan yan ASUU albashin aikin da basu yi ba
- A Oktoba ne aka biya malaman jami'ar da suka shafe watanni suna yajin aiki rabin albashin watan lamarin da ya dawo da hannu agogo baya tsakaninsu da FG
- Ministan ilimi, Adamu Adamu ya ce gwamnatin tarayya ta ce sam ba za ta biya aikin da ba'a yi ba
Abuja - Gwamnatin tarayya ta jadadda cewa ba za a biya malaman jami’a albashin aikin da basu yi ba kamar yadda yake a tsarin ‘babu aiki babu biya’ Daily Trust ta rahoto.
Ministan ilimi, Malam Adamu Adamu, ya bayyana haka yayin da yake martani ga zanga-zangar kungiyar ASUU kan yanayin biyan da aka yi masu a watan Oktoba.
Kungiyar ASUU, wacce ta shiga yajin aiki a watan Fabrairu ta janye yajin aikin a watan Oktoba bayan kakakin majalisar wakilai, Hon. Femi Gbajabiamila ya shiga tsakani.
Gwamnati ba za ta biya aikin da ba a yi ba
Sai dai kuma, mambobin kungiyar sun samu rabin albashi a karshen watan Oktoba, lamarin da bai yiwa malaman jami’ar dadi ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A ranar Laraba, manema labarai na fadar shugaban kasa sun zanta da ministan bayan taron majalisar zartarwa wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a Villa, Abuja.
Da yake martani, Adamu ya ce matsayin gwamnatin tarayya shine ne ba za a biya Lakcarorin albashin aikin da basu yi ba.
Babu mai mayar da malaman jami'a ma'aikatan wucin-gadi, ministan ilimi
Ministan ya kuma yi martani ga zargin da shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodoke yayi cewa biyan da aka yiwa malaman wani yunkuri ne na mayar da su ma’aikatan wucin-gadi.
Adamu ya ce:
“Babu wanda zai iya mayar da malaman jami’a ma’aikatan wucin-gadi.”
Da aka fada masa cewa lakcarorin na barazanar tafiya yajin aikin kwana daya don yin zanga-zanga ga matakin gwamnati, Adamu ya ce shi bai da masaniya, Nigerian Tribune ta rahoto.
A baya mun ji cewa malaman Asuu sun yiwa gwamnati wankin babban bargo kan rashin biyansu cikakken albashi a watan da ya gabata.
Asali: Legit.ng