Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP a Jihar Abiya, Ndidi Okereke, Ya Mutu

Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP a Jihar Abiya, Ndidi Okereke, Ya Mutu

  • Allah ya yi wa tsohon shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Abiya, Chief Ndid Okereke, rasuwa da safiyar Litinin
  • A wata sanarwa da jam'iyyar PDP ta fitar, ta yi ta'aziyya ga iyalan mamacin kuma ta ɗage shirye-shiryen data tsara yau Talata
  • Gwamnan Abiya, Okezie Ikpeazu, ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin da ɗaukacin al'ummar yankinsa

Abia - Tsohon shugaban jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Abiya, Chief Ndidi Okereke, ya rigamu gidan gaskiya.

Ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Litinin a cewar wata sanarwa da mataimakin shugaban jam'iyyar reshen arewacin Abiya kuma muƙaddashin kakakin PDP na jiha, Elder Abraham Amah, ya fitar.

PDP a Jihar Abiya.
Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP a Jihar Abiya, Ndidi Okereke, Ya Mutu Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa har yanzun ba'a bayyana musabbabin abinda ya yi ajalinsa ba amma sanarwan tace ya mutu ne ba zato ba tsammani.

Kara karanta wannan

2023: 'Komai Ya Zo Karshe' Bukola Saraki Ya Magantu Kan Sasanta Atiku da Wike a PDP

An tattaro cewa marigayi Okereke ya rike kujerar shugaban jam'iyyar PDP a jihar Abiya lokacin da marigayi Prince Vincent Ogbulafor, wanda ya mutu kwanan nan, ke matsayin shugaban PDP na ƙasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka zalika marigayi Chief Okereke, wanda ya fito daga Isuochi, ƙaramar hukumar Umunneochi a Abiya, ya kasance tsohon shugaban majalisar Cibiyar Lafiya ta tarayya (FMC) Umuahia.

Jam'iyyar PDP ta yi rashi

Jam'iyyar PDP zata yi babbar kewar Marigayi Okereke, wanda ta ayyana shi da kadara mai girma.

Sanarwan tace:

"Mutuwar Chief Okereke ba zato ba tsammani babban rashi ne ga iyalansa, mutanen yankin Umunneochi, arewacin Abiya, jihar Abiya da baki ɗaya 'ya'yan PDP kuma kowa zai yi kewarsa."
"Da zuciya mai nauyi shugaban PDP a Abiya, Alwell Asiforo Okere, a madadin jam'iyya baki ɗaya na sanar da rasuwar ɗaya daga cikin mutanen kirki kuma tsohon shugaba, Chief Ndid Okereke, wanda ya rasu da safiyar Litinin."

Kara karanta wannan

Wani Gwamna Ya Jingine Tinubu, Atiku da Peter Obi, Ya Faɗi Wanda Yake Goyon Bayan Ya Gaji Buhari a 2023

Bugu da kari, PDP ta sanar da ɗage shirye-shiryen da ta tsara gudanarwa ranar Talata domin zaman makoki da jimamin wannan rashi.

Gwamnan jihar ya jajanta mutuwa

Gwamna Okezie Ikpeazu ya kaɗu da takaicin jin labarin rasuwar a wata sanarwa da sakataren watsa labaransa, Onyebuchi Ememanka, ya fitar.

Gwamnan ya ayyana marigayi Okereke da,"Ɗan siyasa na ajin farko, shugaba kuma cikakken ɗan jihar Abiya."

Ya kuma miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin da kuma ɗaukacin al'ummar yankin ƙaramar hukumar Umunneochi.

A wani labarin kuma Ana Fargabar Da Yawa Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Bude Wuta a Shingen Yan Sanda

Bayanai sun nuna cewa jami'an tsaro sun yi kokarin maida martani bayan sun ɗauki matsaya kuma suka canza kakin dake jikinsu.

Mutane sun shiga tsahin hankali sakamakon ɗauki ba daɗin da aka yi tsakanin jami'an tsaro da maharan a yankin Ihiala na jihar Anambra.

Asali: Legit.ng

Online view pixel