Bidiyon Yara Kanana Suna Neman Na Kai da Adaidaita Sahu ya Taba Zukata

Bidiyon Yara Kanana Suna Neman Na Kai da Adaidaita Sahu ya Taba Zukata

  • Wani bidiyo dake bayyana kananan yara dake tuka Keke Napep wanda ke dankare da fiyo wota ya taba zukatan jama’a
  • A bidiyon TikTok da Anuoluwapo ya wallafa, an ga yaron sun kage a titi mara kyau kuma daya daga cikinsu wanda ke tukin ya sauko yana tura Keken
  • Martani daban-daban sun biyo bayan bidiyon wanda aka wallafa kuma ya samu jinjina sama da 500 a dandalin sada zumuntar

Wani bidiyon TikTok ya bayyana yara kanana biyu suna tuka Keke Napep dankare da fiyo wota ya taba zukatan jama’a.

Bidiyon Yara masu Napep
Bidiyon Yara Kanana Suna Neman Na Kai da Adaidaita Sahu ya Taba Zukata. Hoto daga @Anuowupou
Asali: UGC

Yayin da daya daga cikin yaran ke kula da tuka adaidaita sahun, dayan ya zauna a bangaren fasinja a gaban Keken.

A bidiyon da wani ma’abocin amfani da TikTok din mai suna Anuoluwapo ya wallafa, an ga yaran suna fama da titi mara kyau kuma suna neman fito da adaidaita sahun.

Kara karanta wannan

Magidanci Ya Dinga Kuka da Hawaye Bayan Caca ta Lashe Kudin Makarantar Yaransa

Daya daga cikin yaran maza wanda ke tukin ya sauko kasa inda yake kokarin tura Keken baya don ta fito daga inda ta makale.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan kokarinsa, Keken ta fito kuma sun tuka ta babu bata lokaci inda suka cigaba.

Wani matashi ya kalla idin yaran cike da mamaki inda suke ta kokari da adaidaita sahun. Ba a san ko yaran suna tuka adaidaita sahun don samun kudi bane ko a’a.

Kalla bidiyon a kasa:

Jama’a da yawa kan fada sana’ar da bata dace dasu ba don samun na halas

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto yadda wata mata ke kabo-kabo da mota domin rufawa kanta da iyalinta asiri.

Matar aure ce mai ‘ya’ya wacce tace tana amfani da kudaden wurin hidimtawa ‘ya’yanta har da mijinta.

Tana taimaka masa da wasu manyan bukatu na gida wadanda ya dace a ce shi ne ya dauke su a matsayinsa na namiji.

Kara karanta wannan

Bidiyon Matashi Sanye da Atamfa, Jakarsa, Agogo da Motarsa duk Tsarin Atamfar

Matar auren mai ‘ya’ya ta sanar da cewa tana samun kudi masu wadanda wani ma’aikacin gwamnatin baya samu kuma mijinta ne yayi mata hanyar samun motar da take ja.

Ta kara da bayyana cewa, mijinta yana matukar alfahari da jajircewa tare da neman na kai irin nata ba kadan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

iiq_pixel