Bikin Kirsimeti: Gwamnan APC Ya Umarci a Biya Ma'aikatan Jiharsa Albashin Watanni 2
- Gwamnan jihar Ebonyi ya ba da umarnin kafin 10 ga watan Disamba, 2022, a biya kowane ma'aikaci albashin Nuwamba da Disamba
- Gwamna Umahi ya kuma umarci a ƙara wa ma'aikatan da Bonus ɗin N15,000 kowa, Akanta Janar ya tabbatar an cika umarnin
- Wannan na zuwa ne yayin da mabiya addinin Kirista a Najeriya ke tunkarar bikin Kirsimeti da sabuwar Shekara
Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya ba da umarnin a biya baki ɗaya ma'aikatan jihar albashinsu na watannin Nuwamba da Disamba kafin ranar 10 ga watan Disamba, 2022.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa bayan haka gwamnan na jam'iyyar APC ya yi umarnin a ƙara wa kowane ma'aikaci da N15,000 a matsayin Bonus.
A wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai, Mista Chooks Oko, ya fitar, Umahi ya umarci Ofishin Akanta Janar na jihar, Emeka Nwankwo, ya tabbata an biya waɗan nan kuɗaɗe kafin lokacin.
Yace gwamnatinsa ta ɗauki wannan matakin ne domin baiwa ma'aikata isasshen lokaci da kuɗaɗen da zasu shirya zuwan bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ruwayar The Nation, Sanarwan tace:
"A kokarin gwamnatin Ebonyi na ganin walwala a fuskokin ma'aikatanta, gwamna Dave Umahi, ya ba da umarnin nemo ƙarin buƙatu daga bankuna."
"Buƙatun sun ƙunshi tabbatar da an biya ma'akatan jiha da na kananan hukumoni albashinsu na watannin Nuwamba da Disamba tare da Bonus ɗin Kirsimeti N15,000 daga nan zuwa 10 ga watan Disamba."
Mista Oko ya ƙara da cewa wannan garaɓasa da gwamna ya gwangwaje ma'aikata da shi sun yi dai-dai da sauran kyaututtukan da ya saba kamar Buhun Shinkafa da sauransu.
"Muna fatan wannan garaɓasoshi su ƙara wa ma'aika kwarin guiwa wajen gudanar ayyukansu yadda ake ɓukata."
Gwamna Buni ya naɗa Kantomomi a jihar Yobe
A wani labarin kuma Gwamnan jihar Yobe na APC ya rantsar da shugaban ma'aikata tare da Kantomomin ƙananan hukumomi 17 dake faɗin jihar
Mai Mala Buni, tsohon shugaban kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa, yace ya yi haka ne domin wa'adin zaɓaɓɓun Ciyamomi ya ƙare.
Gwamnan ya kuma roki mutanen da aka ba wannan amana da su jajirce wajen samar da gwamnati mai inganci ga al'ummar yankunansu.
Asali: Legit.ng