Dakarun Sojoji Sun Kashe Gomman 'Yan Bindiga a Jihar Zamfara
- Dakarun Operation Forest Sanity sun yi artabu da yan bindiga a karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara
- Sojojin sun sheka gomman yan bindiga lahira yayin da suka kwato daruruwan babura da dabbobi masu yawan gaske
- Al'ummar garuruwan da ke kananan hukumomin Bukkuyum da Gummi sun cika da farin ciki inda suka garzaya wajen da abun ya faru don ganin fuskokin miyagun da aka kashe
Zamfara - Dakarun sojojin Najeriya sun halaka gomman yan bindiga a wani samame da suka shafe kwanaki biyu suna kaiwa wani daji kusa da wani gari da ake kira Gadar Zaima a karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara, Daily Trust ta rahoto.
Aikin wanda aka yi cikin nasara ya yi sanadiyar kwato babura fiye da guda 100 da kuma shanaye kimanin guda 600 lamarin da ya haifar da gagarumin farin ciki a fadin garuruwan da ke kananan hukumomin Bukkuyum da Gummi.
Sahara Reporters ta kuma rahoto cewa sojojin sun ceto mutane hudu da aka yi garkuwa da su a yayin samamen.
Garuruwan da ke kananan hukumomin Gummi da Bukuyyum sun fuskanci hare-haren yan bindiga
Garuruwan da ke kananan hukumomin biyu sun fuskanci yawan hare-hare da garkuwa da mutane a yan makonnin baya-bayan nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kashe mutane da dama sannan an fatattaki mutanen kauyuka da dama sakamakon mummunan farmakin da madugun yan bindiga mai suna Buzu ya kaddamar.
Mazauna yankin sun bayyana cewa dakarun sun kama wasu guggun yan fashi da makami da suke kora dabbobi masu yawan gaske.
Wani mazaunin yankin mai suna Usman ya ce:
“Yan bindigar na fitowa daga wani gari da ake kira Zugun-Kebbe, a kusa da iyakar jihar Sokoto ta wani daji mai suna Dajin Danmarke lokacin da zazzafan arangamar ya barke.
“An kashe gomman yan bindiga kuma an bar gawarwakinsu zube a wajen da aka yi artabun, kimanin kilomita 1 kusa da hanyar Anka-aki Takwas-Gummi-Zuru. An kashe wasu daga cikin miyagun lokacin da suka dawo kwasar gawarwakin takwarorinsu.
“Na kirga babura fiye da guda 60 da aka kwato daga hannunsu. An gano tulin babura da dabbobi da kwato suna shiga garin Gummi yayin da mazauna yankin ke jinjinawa sojojin.
“An gargadi mutanen da ke zuwa wajen da aka yi arangamar don kallon matattun yan bindigar da su janye yayin da ake tsoron mayakan na iya sake shiri da kuma dawowa.”
Ba a samun ji ta bakin kakakin dakarun Operation Hadarin Daji, Kyaftin Ibrahim Yahaya ba.
Asali: Legit.ng