Bidiyon Wata Babbar Mota Dankare Da Kudi Yan Naira Dubu-dubu Marasa Kyau Daga Arewa

Bidiyon Wata Babbar Mota Dankare Da Kudi Yan Naira Dubu-dubu Marasa Kyau Daga Arewa

  • An gano wata babbar mota da ta lalace dankare da kudade yan naira dubu-dubu a soshiyal midiya
  • A cewar bidiyon, babbar motar ita ce ta uku da aka dankarawa kudade daga wata jihar arewa ana neman inda za a juye su
  • Lamarin na zuwa ne yayin da babban bankin kasa wato CBN ya fara shirin sauya wasu kudade daga cikin takardun naira

Wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya ya nuna wata lalatacciyar babbar mota cike da kudi yan N1,000 daga wata jihar arewa.

Kamar yadda mutanen da ke cikin bidiyon suka bayyana, wannan motar ta kai kimanin watanni biyu a wajen suna neman inda za a juye su.

Mutane da babbar mota
Bidiyon Wata Babbar Mota Dankare Da Kudi Yan Naira Dubu-dubu Marasa Kyau Daga Arewa Hoto: Elijah Ajanu-Ojo
Asali: Facebook

Motar ita ce ta uku dankare da naira

Bidiyon ya nuno takardun nairori musamman yan N1,000 marasa kyau, wanda masu daukar bidiyon suka yi ikirarin cewa an ajiye su ne a wani wuri da ya rubar da su. Yanzu mamalakansu ke neman wurin da za su canja su da dala.

Kara karanta wannan

Bidiyon Shigar Ango Wurin Shagalin Aurensa a Akwatin Gawa Ya Gigita Amarya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakan na zuwa ne a yayin da babban bankin kasa wato CBN ke shirin sauya takardun naira wanda ya kawo tangarda ga kudaden gida a kasuwa.

Ana ta samu bidiyoyi da hotunan kudaden da yan Najeriya suka boye tun daga shekaru 20 da suka wuce suna yawo yayin da CBN ke shirin fito da sabon kudin da aka sauya daga ranar 15 ga watan Disamba 2022.

Yawan naira a kasuwa ya ruguzo da farashin kudin warwas, inda ake siyar da kowani da kan N900 a kasuwar bayan fage sannan N442 kan kowani dala a hukumance.

Kamar yadda ya bayyana a bidiyon, an jiyo daya daga cikinsu na cewa:

"Wannan tsakaninmu da su sai dai Allah ya kawo mana mafita. Wannan kudi ne billahillazi la’ilaha illahuwa, gashi nan yanzu ba wai karya yayi ba wallahi da gaske wallahi tallahi gasu nan a hannuna sune wannan tirelar sun kai kusan watanni biyu a wajen nan.

Kara karanta wannan

Mutane Na Cigaba da Fito da Kudin da Suka Boye, An Gano N200 da Aka Buga Tun 2003

Gasu nan kudi ne tsalala gashi an dandake su a injin kwali sun ruba, gashi mu mun gama rubewa a kasa abun da zamu sa a bakinmu babu, babu yadda zamuyi amma mallam ga kudi ne."

Kalli bidiyon a kasa:

A wani labarin, gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ce zai baiwa hukumar yaki da cin hanci da rashawa damar gudanar da bincike a cikin wani gidansa da ke Abuja.

An dai zargi gwamnan da wasu gwamnoni biyu da boye kudade a gidansu yayin da babban bankin CBN ke shirin sauya fasalin naira.

Sai dai Matawalle ya karyata wannan rahoto inda yace bai da tushe balle makama kuma yunkuri ne na bata masa suna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng