Yadda Wata Budurwa Yar Shekara 18 Ta Kashe Jaririnta Da Wuka Bisa Shawarar Mahaifiyarta Yar Shekara 60

Yadda Wata Budurwa Yar Shekara 18 Ta Kashe Jaririnta Da Wuka Bisa Shawarar Mahaifiyarta Yar Shekara 60

  • Yan sanda a jihar Enugu sun kama wata budurwa yar shekara 18 kan halaka jinjiri da ta haifa a garin Olocha-Adogba a Agwu, karamar hukumar Awgu
  • Binciken da yan sanda suka yi ya nuna cewa budurwar ta halaka jinjirin ne bisa umurnin mahaifiyarta mai suna Christiana Okonkwo, mai shekaru 60
  • Kwamishinan yan sandan jihar Enugu Ahmed Ammani ya yi tir da lamarin ya kuma ce za a yi bincike a gurfanar da wadanda ake zargi kuma ya shawarci matan garin su yi zanga-zangar nuna kyamar lamarin

Enugu - Rundunar yan sanda ta jihar Enugu a ranar Juma'a ta ce ta kashe kama wata matashiya yar shekara 18 kan hada baki da kashe jinjiranta a garin Olocha-Adogba a Agwu, karamar hukumar Awgu na jihar, rahoton The Punch.

Yan sandan sun ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin misalin karfe 1 na rana lokacin da wacce ake zargin mai suna Ada Joy Okonkwo, mai shekaru 18, ta haihu sannan ta hada baki da mahaifiyarta, Christiana Okonkwo, mai shekaru 60, don kashe jinjirin.

Kara karanta wannan

Wani Matashi Ɗanlami Mai Shekara 25 Ya Jefe Mahaifinsa Har Lahira A Wata Fitacciyar Jihar Arewacin Najeriya

Wacce suka kashe da
Wata Budurwa Yar Najeriya Ta Kashe Jaririnta Da Wuka Bisa Shawarar Mahaifiyarta. Hoto: @SaharaReporters.
Asali: Twitter

A wani sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar, Daniel Ndukwe, kwamishinan yan sandan jihar Ahmed Ammani, ya bada umurnin sashin SCID ta Enugu ta yi cikakken bincike kan lamarin, SaharaReporters ta rahoto.

Kwamishinan ya kuma yi tir da lamarin ya bayyana shi a matsayin abin bakin ciki

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar ta ce:

"Binciken farko ya nuna cewa mahaifiyar jinjirin ta yi amfani da wukar kicin ta caka masa ya mutu bisa shawaran mahaifiyarta," ya kara da cewa lamarin ya faru "jim kadan bayan ta haifi jinjirin."

Kakakin yan sandan ya ce an kai jinjirin asibiti kuma likitoci sun tabbatar ya rasu, kuma an ajiye gawarsa a dakin ajiye gawa don gwajin musababin mutuwa.

Kwamishinan yan sandan ya shawarci matan garin su yi zanga-zangan lumana

Kazalika, Ndukwe ya ce kwamishinan ya yi kira ga mazauna garin, musamman mata su yi tattaki na lumana, don nuna bacin ransu da kyama kan lamarin, kuma su cigaba da zama lafiya, su guji abin da zai kawo tabarbarewar doka da oda a garin.

Kara karanta wannan

An Gurfanar Da Abubakar A Kotu Kan Satar Burodi A Kaduna

Ya yi kira gare su da su bada goyon baya yayin da za a gudanar da bincike mai zurfi tare da gurfanar da su gaban kuliya.

Wani Matashi Ɗanlami Mai Shekara 25 Ya Jefe Mahaifinsa Har Lahira A Wata Fitacciyar Jihar Arewacin Najeriya

A wani rahoton, rundunar yan sanda ta jihar Filato a ranar Juma'a ta tabbatar da kama wani Bernard Danlami, mai shekara 25 kan kashe mahaifinsa a karamar hukumar Mangu, rahoton The Punch.

Kwamishinan yan sandan jihar Filato, Onyeka Bartholomew, ya tabbatarwa manema labarai hakan yayin da ya ke jawabi kan ayyukan hukumar a hedkwatar yan sanda a Jos, ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164