Jami'an Tsaron Najeriya Sun Samu Nasarar Kashe Kasurgumin Dan Bindiga Dogo Maikasuwa

Jami'an Tsaron Najeriya Sun Samu Nasarar Kashe Kasurgumin Dan Bindiga Dogo Maikasuwa

  • Gwamnatin Kaduna ta yi farin cikin samun labarin kisan kasurgumin dan bindigan da ya addabi Kaduna
  • Dogo Maikasuwa ya shahara da hallaka mutane da yayi garkuwa da su idan aka bata masa lokaci
  • Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da yan bindiga masu garkuwa da mutane suka addaba

Kaduna - Jami'an tsaron Najeriya sun samu nasarar kawo karshen rayuwar shahrarren dan bindiga, ‘Dogo Maikasuwa’ wanda ya addabi al'ummar jihar Kaduna.

Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar ranar Juma'a kuma Legit Hausa ta samu.

A cewarsa, Dogo Maikasuwa, wanda aka fi sani da ‘Dogo Maimillion' ya addabi babban titin Kaduna zuwa Kachia da kuma al'ummar Chikun-Kajuru.

Yace:

"Yana daya daga cikin yan bindigan da suka fi hadari kuma suka addabi al'ummar yankin."

Kara karanta wannan

Muna sane: IGP ya fadi matakin da 'yan sanda ke dauka bisa harin da aka kai kan tawagar Atiku

"Ya shahara da mugunta kuma ya kasance mai kashe wadanda ya sace idan akayi jinkirin biyan kudin fansa ko kuma aka biya kudin da bai gamsu da su ba."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"A ranar da dubunsa ta kare, ya shiga tarkon dakaru tare da yaransa a Gengere-Kaso a iyakan Chikun da Kajuru."
Aruwan
Jami'an Tsaron Najeriya Sun Samu Nasarar Kashe Kasurgumin Dan Bindiga Dogo Maikasuwa Hoto: @samuelaruwan
Asali: Twitter

Aruwan ya kara da cewa jami'an tsaron sun samu nasarar hallakashi tare da bindigarsa, babura biyu da rigar Soji.

Ya ce sauran yaransa sun samu nasarar tsira da raunukan amma daya daga cikinsu ya mutu kuma sun tafi da gawarsa.

Gwamna El-Rufa'i Ya yiwa Almajihar Sama Da 2500 Sha Tara Ta Arziki

Gwamnatin Jihar Kaduna tare da hadin gwiwar Asusun Kula Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) a ranar Laraba, ta kaddamar da rabon kudade ga yaran Almajirai a karkashin shirin ‘Children Street Programme’.

Kara karanta wannan

Tsagerun 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Kazamin Hari a Wata Jihar Arewa, Sun Halaka Mutum 2

A karkashin shirin, Almajirai 2,674 da aka maida su ga iyaytensu ne, za su karbi kudi Naira 5,000 don shiga makaranta ko dan koyan sana'a

Da take jawabi a wajen taron a Kaduna, mataimakiyar gwamnan jihar, Dakta Hadiza Sabuwa, wacce ta wakilici gwamna Nasir El-Rufai, ta ce ilimi da jin dadin yara abu ne mai matukar kima ga gwamnatin su ta bawa a kokarinta na bunkasa rayuwar dan Adam.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida